Majalisar Koli ta Najeriya wato Council of State, ta bukaci Babban Bankin Najeriya CBN da ya wadata kasar da sabbin takardun Naira ko kuma ya bayar da damar ci gaba da amfani da tsofaffin kudade.
Wannan dai na zuwa ne bayan da Majalisar ta kammala wani taron gaggawa a Fadar shugaban kasar da ke Abuja inda ta bukaci babban bankin kasar, CBN ya samar da karin sababbin takardun kudi domin saukaka wa al’ummar kasar halin da suke ciki.
- Ukraine ta lalata wa Rasha makamai masu linzami biyar
- Canjin Kudi: Ganduje ya maka Buhari a Kotun Koli
A cewar majalisar, idan sababbin kudin ba za su samu ba, to CBN ya koma bai wa jama’a tsofaffin takardun kudin.
Majalisar – wadda ke karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari – ta kira taron ne domin tattaunawa kan halin da kasar ke ciki a yanzu da ta ke tunkarar babban zabe.
Majalisar ta kunshi tsofaffin shugabannin Najeriya da shugabannin Majalisar Dattawa da na Wakilai da wasu ministoci da kuma gwamnonin kasar.
Ta kuma ce duk da matsalolin da ake fuskanta, tana goyon bayan tsarin Babban Bankin na sake fasalin naira.
Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku wanda ya yi wa manema labarai karin bayani ya ce, “An shawarci CBN ya wadata kasar da sabbin takardun kudin ga jama’a ko kuma a sake fito da tsofaffin kudi domin kawo karshen wahalar da jama’a ke fuskanta.”
A waje daya kuma Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wa majalisar bayanai game da shirye-shiryen Babban Zaben kasar inda ya nuna cewa hukumar ta kammala shirin gudanar da zabukan da za a yi daga karshen wannan watan.
Shi ma Babban Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya, Usman Alkali Baba, ya yi wa majalisar bayanai game da irin matakan tsaro da suke shirin dauka a lokacin zaben.