Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankuna su fara ba wa ’yan Najeriya sabbin takardun Naira da aka sauya wa fasali a saman kanta.
Umarnin na CBN ya kayyadde ba wa kowane kwastoma Naira 20,000 na sabbin kudaden a kullum, kamar yadda Darakan yada Labaran bankin, Osita Nwanisobi, ya sanar a safiyar Alhamis.
Hakan na zuwa ne bayan guna-gunin ’yan Najeriya kan karancin sabbin takardun kudaden a hannunsu, alhali sun riga sun kai akasarin tsoffin da ke hannunsu bankuna domin gudun cikar wa’adin tsoffin da CBN ya sanar a baya.
Batun karancin sabbin takardun kudaden dai ya kawo cikas ga harkokin kasuwanci, a yayin da ’yan Najeriya ke shafe awanni suna bin layi domin cira daga ATM, inda a karshe ma wasu ba sa samu.
Hakan ya ba da dama ga masu harkar POS, inda suke cin kasuwa, tare da kari a kan cajin da suke karba a kan masu neman sabbin kudaden a hannunsu.
Daga baya hatta tsoffin kudin rububin neman su ake yi, damar da masu hada-hadar kudi ke amfani da ita wajen tatsar al’umma.
CBN dai sun nuna damuwa game da ayyuka masu sayar da sabbin kudaden da kuma masu yin liki da kudi a wuraren bukukuwa.
Sun kuma jaddada cewa za su ci gaba da aiki da hadin gwiwar hukumomin FIRS, EFCC da NFIU domin maganin masu yin hakan.