✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya umarci bankuna su ci gaba da karbar tsoffin takardun N1,000 da N500

Umarnin na zuwa ne bayan kalaman Fadar Shugaban Kasa kan lamarin

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya umarci bankunan kasuwanci da su ci gaba da karbar tsofaffin takardun kudi na N1,000 da N500 har nan da ranar 31 ga watan Disamba.

Umarnin na zuwa ne bayan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce ba da yawunsa CBN da Ministan Shari’a suka ki bin umarnin Kotun Koli kan batun ba.

CBN ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da Kakakinsa, Isa Abdulmumin ya fitar da daren Litinin.

Ya ce umarnin ya dace ne da hukuncin Kotun Koli da ya nemi a ci gaba da amfani da kudin har zuwa karshen shekarar 2023.

“Dogaro al’adar bankin ta yin biyayya ga hukuncin kotu da kuma bin doka da oda da gwamnatin Shugaba Buhari ta sunnanta, da kuma ayyukan CBN, a matsayinsa na jagoran tafiyar da harkokin kudi a Najeriya, muna umartar bankunan kasuwanci da su bi wannan hukuncin na Kotun Koli na ranar uku ga watan Maris, 2023,” in ji sanarwar.

Ta kuma kara da cewa, “CBN ya gana da kwamitin masu bankuna, sannan ya umarci a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N1,000 da N500 da kuma N200 tare da sababbin a lokaci daya, har zuwa ranar 31 ga watan Disamban 2023.

“Saboda haka, ana umartar duk wadanda abin ya shafa da su bi wannan umarnin,” in ji CBN.