Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce ya tura wa bankunan kasar takardun kudaden naira don su wadatar da al’ummar kasar da ke fuskantar karancin kudi a hannunsu.
Mukaddashin Shugaban Sashen Yada Bayanai na bankin, Dokta Isa Abdulmumin ne ya bayyana hakan a cikin sanarwar da ya fitar.
- Akwai gwamnonin da za mu kama da zarar wa’adinsu ya kare — EFCC
- Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da zaben Ademola Adeleke
A wannan Juma’ar bankin na CBN ya fitar da sanarwar yana mai umartar bankunan da su yi aiki har a karshen mako don kudin ya kai ga hannun jama’a.
“CBN na ba da umurni ga bankuna da su loda na’urorin cire kudi da takardun naira, su kuma bude hanyar karbar kudaden a cikin banki har zuwa cikin karshen mako.”
’Yan Najeriya sun kwashe tsawon lokaci suna fama da karancin takardun kudi tun bayan da aka sauya fasalin naira 200, 500 da 1,000 a bara.
Lamarin ya haifar da tarnaki ga harkokin kasuwanci a sassan kasar tun daga karshen shekarar da ta gabata.
A watan da ya gabata kotun kolin Najeriya ta ce a ci gaba da amfani da tsoffin kudaden naira har zuwa karshen 2023.