Babban bankin Najeriya (CBN) ya kara wa’adin kwana 10 kan lokacin da ya sanya na daina karbar tsofaffin takardun kudi a baya.
Cikin wata sanarwa da Gwamnan bankin, Godwin Emefiele ya fitar ranar Lahadi, ya ce Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ne ya amince da tsawaita lokacin zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu.
- ISWAP ta kori ’yan Boko Haram daga zama ’ya’yanta kan zargin zagon kasa
- INEC ta sake kara wa’adin karbar katin zabe
Emefiele, wanda yanzu haka yake Daura, mahaifar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
Gabanin sanarwar dai, Emefiele ya gana da Shugaban, inda a nan ce ya samu izinin kara sabon wa’adin.
Ya ce karin zai kasance dama ga ’yan Najeriyar da ba su sami damar canza kudinsu ba, yanzu su samu su yi haka.
Sai dai bankin ya gargadi jama’a da su yi amfani da damar kada su shantake daga baya su nemi kari.
A bara ne dai babban bankin ya sanar da sauya fasalin takardun kudi na N1,000 da N500 da kuma N200, a cikin irin matakan da yake dauka na rage yawan amfani da tsabar kudi a tsakanin al’umma.