Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kara farashin canjin Dala da yake bayarwa da Naira 170, daga N461 zuwa Naira 631.
A hannu guda kuma Aminiya ta gano cewa farashin canjin Dalar ya yi faduwar bakar tasa a kasuwar bayan fage a Kano da Abuja a yammacin ranar Laraba.
CBN ya dauki matakin ne kwana biyu bayan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin daidaita farashin canji domin farfaɗo da tattalin arziki.
A jawabinsa na kama aiki a matsayin shugaban kasar Najeriya na 16 ne Tinubu ya ce, “Tsarin kudin Najeriya na bukatar gyara kuma doke CBN ya tabbatar da farashin canji na bai-daya.
- Farashin kaya ya yi tashin gwauron zabo bayan cire tallafin mai
- Yadda hukumomin gwamnati suka salwantar da tiriliyan 3.8 a mulkin Buhari —Rahoto
“Hakan zai kawo karshen dibar karan mahaukaciya da ake yi wa farashin, da haka ne za a samu damar amfani da kudaden a bangaren masana’antu da samar da kayan aiki da wutar lantarki da kuma tattalin arziki.”
A ranar Talata da Tinubu ya fara shiga ofis ya yi wata ganawar sirri da Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, a Fadar Shugaban Kasa.
Amma Aminiya ta samu bayani daga wata majiya mai tushe cewa batun canjin kudi na daga cikin abubuwan da suka tattauna a zaman.
Aminiya ta gano cewa a ranar Laraba CBN ya bai wa bankuna Dala domin ba wa kwastomominsu a kan Naira N631 kuma yawanci sun samu kudaden kasar waje da suka bukata.
Wani wanda ya nemi canjin Dala a wani banki ya tabbatar mana cewa ya samu Dalan da ya bukata, amma a kan Naira 631, sabanin N461.6 da aka saba.
Mataimakin da CBN ya dauka ya sa Dala ya yi faduwar bakar tasa daga N750 zuwa N745 a kasuwar bayan fage a Kano da Abuja a yammacin ranar Laraba.
Faduwar Naira biyar a rana guda da Dala ta yi a rana guda ita ce mafi girma a tsawon shekara guda.
Kafin furucin Tinubu kan canjin Dala, darajar Dala ta karu daga Naira762 zuwa N775 a ranar Juma’a a Legas, in ji wani dan canji a can mai suba Umar Salisu.
Ya ce irin hakan ne ya yi faruwa a cikin makon da ya gabata, bayan an dan samu daidaito a farko-farkon shekara.
Akan samu tazara mai yawa tsakanin farashin canji na gwamnati da na kasuwar bayan fage, wanda masana ke gani ya ba wa ’yan canji damar tatsar jama’a ta hanyar sanya farashin da suka ga dama.
Daga shekarar 2020 zuwa yanzu bambancin ya karu daga Naira 100 zuwa N400, bayan da Dala ta kai N880 a bara, kafin ta sauka daga baya.
Yawan tazar ne ya sa CBN ya bullo da hanyoyin taka wa ’yan canji na bayan fage burki, ciki har da daina ba su kudaden kasashen waje.