Babban Bankin Najeriya (CBN) ya haramta wa bankuna bai wa kwastomominsu sabbin takardun Naira a saman kanta.
Banckin yce maimakon haka, bankunan su tabbatar sun loda sabbin takardun kudin a injinan ATM don su wadatu a hannun ’yan Najeria kafin wa’adin 31 ga Janairu, 2023 da tsoffin takardun kudin za su daina aiki.
- Shekara 1 da rasuwar Sheikh Ahmad Bamba
- Rikicin Limanci ya hana Sallar Juma’a a Masallacin Dokta Ahmad Bamba
- Matashi ya yi garkuwa da mahaifinsa, ya karbi fansar N2.5m
Jaridar Punch ta ruwaito wata majiyar na cewa, “CBN ya ba mu umarnin daina ba wa kwastomomi sabbin takardun N200 da N500 da kuma N1000 ta kanta.
“Maimakon haka, ya bukaci a loda kudin a wadace a injinan ATM don jama’a su samu su cire.
“Nan take ake bukatar aiwatar da wannan umarni.”
Punch ta ce ta gano cewa CBN ya ba da umarnin ne ranar Laraba tare da bukatar a fara aiki da shi nan take.
Sai dai duk da haka, wasu bankuna sun ki bin umarnin na CBN sakamakon karancin sabbin tarkadun Naira, ballantana su su loda a ATM don amfanin jama’a.
A cewar majiyar, karancin sabbin takardun Naira ya sa tilasa bankuna ke gwama sabbi da tsoffin takardun N1,000 da N500 suna sakawa a ATM kafin lamurra su daidaita.