✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN ya ba Jihar Neja tallafin noman biliyan N1.5

Gwamnatin Jihar Neja ta samu tallafin Naira biliyan 1.5 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin bunkasa noman shinkafa da wake da masara da waken suya…

Gwamnatin Jihar Neja ta samu tallafin Naira biliyan 1.5 daga Babban Bankin Najeriya (CBN) domin bunkasa noman shinkafa da wake da masara da waken suya a jihar.

Tallafin wani bangare ne na Shirin Bunkasa Harkar Noma na CBN na shekarar 2018.

Kwamishinan Noman Jihar, Haruna Dukku ya ce matasa 10,000 ’yan shekara 18 zuwa 35 daga sassan jihar za su ci gajiyar ayyukan noma iri-iri, musamman domin samar a abubuwan more rayuwa a yankunansu.

Kwamishinan ya ce bunkasa harkar noma na daga cikin manufofin gwamanatin jihar, shi ya sa take ba wa bangaren kulawar da ta dace.

Ya ce za a gyara kamfanin casar shinkafa da ke garin Bida wanda kasar Koriya ta gina.

Dukku ya ce za a yi gyaran ne bayan Ofishin Jakadancin kasar Koriya ya nuna damuwa game da watsi da aka yi da kamfanin mai shekara 45.

Ya ci gaba da cewa an bayar da aikin ga babban kamfanin sarrafa shinkafana Elephant Group mai rassa takwaa a Najeriya, kuma nan gaba kadan za a kammala kulla yarjejeniyar.