✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CBN na mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudade – ACF

ACF ta yi kira ga Gwamnan bankin da ya duba shawarwarinsu da kyakkyawar manufa.

Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF) ta aike da wata wasika ga Gwamnan Babban Bankin Najeriya na CBN, Godwin Emefiele bisa zargin mayar da ’yan Arewa saniyar ware a harkokin kudaden bankin.

ACF, a cikin wasikar wacce shugabanta, Audu Ogbeh ya sanyawa hannu ta koka kan yadda ta ce ba lallai sabuwar manufar hada-hadar kudade ta masu kananan sana’o’i ta yi tasiri a yankin ba.

Ogbeh ya ce hatta kananan bankunan da aka dorawa alhakin gudanar da irin wadannan harkokin kudaden ba sa yin abinda ya kamata a Arewacin Najeriya.

Ya kuma yi Allah-wadai da sabuwar ka’idar da CBN ya fitar a matsayin mafi karancin jari ga kananan bankuna, inda ya ce irinsu guda 310 ne kacal suke aiki a Arewa.

Audu Ogbeh, wanda tsohon Ministan Gona ne ya kuma yabawa rawar da bankin yake takawa wajen yaki da talauci, inda ya yi kira ga Gwamnan bankin da ya duba shawarwarinsu da kyakkyawar manufa.

Wasikar ta ce, “Duba na tsanaki ga ka’idojin da CBN ya shimfida, zai kai ga durkushewar kananan bankuna da dama da yanzu suke aiki a Arewa

“Hakan zai sa mutanen Arewa da dama su kara zama saniyar ware, ya kara ta’azzara barnar annobar COVID-19, ya kara talauci sannan kuma ya dada matsalar tsaron da muke ciki a yankinmu”.

Ya kuma soki lamirin Babban Bankin kan wa’adin watan Afrilun 2021 ga kananan bankunan domin su sabunta jarinsu, inda ya bayar da shawarar a mayar da wa’adin zuwa 2025.

Ogbeh ya ce hakan ne kadai zai ba bankunan damar samo isassun kudaden, musamman la’akari da irin mawuyacin halin tattalin arzikin da ake ciki.