Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA), Manjo-Janar Mohammed Monguno (mai murabus), ya ce canjin kudi da tsarin rashin ta’ammali da tsabar kudi na Babban Bankin Najeriya (CBN), za su shafi ayyukan sojoji muddin ba a dauki matakan da suka dace ba.
Monguno ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci a gaban Majalisar Wakilai kan batun sabbin tsare-tsaren na CBN ranar Alhamis a Abuja.
- NAJERIYA A YAU: Karancin Kudi Na Sa Farashin Kayan Masarufi Faduwa
- ’Yan jaridar bogi sun shiga hannu kan damfara da ‘transfer’ ta bogi
“Saboda muhimmancin wasu bayanan game da tsaro, ba komai za mu bayyana manema labarai ba,” in ji shi.
Ya yi wadannan kalaman ne ta bakin wakilinsa, Rear Admiral Abubakar Mustapha, inda ya ce, “Ko a manyan kasashen duniya, wadannan matakai ka iya shafar sojoji muddin ba a tafiyar da su yadda ya dace ba.
“NSA na nufin dakarunmu da aka tura aiki a wuraren da babu halin yin amfani da hanyoyin hada-hadar kudi na zamani.
“Yana da kyau kwamitin ya zauna ya samar da hanyoyi masu bulewa domin magance wadannan matsaloli.”
Tun da fari, shugaban kwamitin, Ado Doguwa, ya ce da ma dai kwamitin na da ra’ayin duba irin tasirin da tsarin zai yi kan sha’anin tsaron kasa da sauran fannoni.
A karshe, ya dake ci gaba da zaman zuwa ranar Juma’a, 10 ga Fabrairu don ganawa da Ministar Kudi da sauran masu ruwa da tsaki.