✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Canjin Kudi Ya Kawo Koma-Baya Ga Noman Rani —Adamu Tinda

Manoman rani a kauyen Tinda da ke Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe sun koka kan yadda karancin kudi a hannu ya jawo musu asara…

Manoman rani a kauyen Tinda da ke Karamar Hukumar Kwami a Jihar Gombe sun koka kan yadda karancin kudi a hannu ya jawo musu asara a harkar noman su na rani.

Wani wanda ke noman ranin kankana da kubewa da Sweet Melon da bambus a yankin, Muhammad Adamu Tinda, ya ce tsarin takaita amfani da tsabar kudi da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kawo ya sa suna ji suna gani abin da suka noma suna lalacewa saboda rashin masu saya kudi a hannu, ga shi kuma su mutanen kauye ne, ba su iya harkar banki ba.

Ya bayyana cewa saboda karancin kudi a hannu gonar da aka sayar Naira miliyan daya a bara, a bana da kyar aka sayar da ita Naira dubu dari, wata kuma da aka sayar dubu dari bakwai an sayar da ita dubu dari da hamsin.

Muhammad Adamu ya ce, “Kadada takwas nake nomawa kuma Alhamdulillah ana samun alheri a noman shi ya sa muka rungumi noman gadan-gadan.”

Amma ya ce yanzu haka suna neman masu sayen kayan da suka noma babu su saboda karancin kudi, sai a ’yan kwana-kwanan nan da aka dan fara samun kudi darajar amfanin ya fara farfadowa.

A cewarsa, a wannan karon noman ya kada su saboda halin canjin kudin ga kuma karancin ruwan kogi domin ruwan ya janye ya yi nisa kuma kayan ban ruwa sun yi tsada.

Adamu, ya yi kira ga gwamnati da ta kawo musu tallafin taki da injunan ban ruwa da maganin feshi sannan kuma a tona musu kananan tafkuna da zai saukake musu ban ruwa.

Daga nan sai ya bukaci a samar musu da hanya domin garin na Tinda babu hanya wanda hakan ya sa ba sa iya yin noman damina sai na rani saboda a lokacin damunan garin baya shiguwa saboda karali ne.