✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi: Majalisa ta yi barazanar sa wa a kamo mata Emefiele

Majalisar ta ce tana da hurumin da za ta sa 'yan sanda su kamo mata shi

Majalisar Wakilann Najeriya ta yi barazanar amfani da karfin iko wajen sanya wa a kamo mata Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele saboda kin amsa gayyatar da ta yi masa.

Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis, kan yadda Emefelen ya yi biris da gayyatar da majalisar ta yi masa karo na biyu don amsa tambayoyi daga kwamitin Alhassan Ado Doguwa.

Cikin wata wasika da CBN din ya aika wa majalisar, ya ba da hanzarin cewa Emefiele ba zai samu damar halartar zaman majalisar na ranar Alhamis ba.

“An gayyaci Gwamnan Babban Bankin da shugabannin bankunan Najeriya ne don ba da dalilansu na gaza raba sabbin takardun kudi kafin ranar 31 ga watan Janairu da tsofaffi za su daina aiki a hukumance.

“Majalisa ta kirkiri sabon kwarya-kwaryar kwamiti karkashin jagorancin Shugaban Masu Rinjayenta, Alhassan Ado Doguwa, don zama da su, amma babu wani jami ’i daga CBN da ya halarta. Wannan bai dace ba ko kadan!

“Bayanai na nuna cewa rabon sababbin takardar kudin da ake yi na cike da matsaloli. Kuma sakamakon wannan gazawar ba zai haifar da sakamako mai kyau ba ga ’yan Najeriya, musamma ma bangaren gudanr da harkokin kasuwancinsu.

“Kin amsa gayyatar majalisar na nuna rashin mutunta rayuwar al’ummar Najeriyar da sune abokan huldarsu da suka yi. Haka nan kuma cin fuska ne ga hukuma da ita kanta majalisar.

“Don haka zan yi amfani da wannan damar wajen sanar da CBN cewa karksshin sashi na 89(1)(d) da na 19 (2)(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya, da karfin ikon majalisar, tana da ikon bai wa Sifeta Janar na ’yan sandan Najeriya umarnin kamo mata Emefele da saura shugabannin bankin, don amsa gayyatar,” in ji Gbajabiamila.