✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Canjin kudi: El-Rufa’i ya sake maka Buhari a kotu saboda kin bin umarnin kotu

Canjin kudi: El-Rufa'i ya sake maka Buhari a kotu saboda kin bin umarnin kotu

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sake maka Gwamnatin Tarayya da kuma Babban Bankin Najeriya (CBN) a gaban kotu kan wa’adin canjin kudi, saboda abin da suka kira bijire wa umarnin kotun da gwamnatin ta yi.

Lauya gwamnatin, Abdulhakeem Mustapha (SAN) ne ya shigar da karar a madadin gwamnatin ranar Litinin.

A zaman kotun da Mai Shari’a Inynag Okoro ya jagoranta, Mustapha ya ja hankalin kotu kan yadda gwamnatin tarayya tayi watsi da umarnin kara wa’adin daina karbar tsoffin takardun kudin na N1,000, da N500, da kuma N200.

Sai dai lauyan gwamnati Kanu Agabi (SAN) ya musanta zargin, duk da dagewar lauyan masu kara.

A nata bangaren kotun ta ba da umarnin tattara bayanan da suka kamata na shigar da kara a ranar Juma’a, da kuma gabatar da martani ranar Litinin, don fara zaman sauraro ranar Laraba.

Kazalika Emmanuel ya bukaci Gwamnatin jihar Ribas ta gabatar da ta ta karar daban.

Haka kuma lauyan Gwamnatin Kano Sunusi Musa shi ma ya nemi matsar da ta su karar da ke kalubalantar ikon gwamnatin tarayya na tilasta wa ’yan kasa aiwatar da dokar,  ba tare da sahalewar Majalisun Dokokin kasa ba.

Sai dai Alkalin kotun Koke O Okoro ya shawarci Gwamnonin Ribas da Kano su hade ta su karar da wadanda aka riga aka shigar, daga nan kuma kotun ta sanya ranar Laraba 20 ga Fabrairu a matsayin ranar fara sauraron kararrakin.