Dan takarar Shugaban Kasa a Jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya ce a matsayinsa na da ga ’yar kasuwa hakan ya ba shi damar fahimtar matsalar da canjin kudi ya haifar a cikin al’umma.
A lokuta da dama dan takarar ya bayyana rashin dacewar sabon tsarin, inda ya ce a matsayinsa na wanda ya tashi a cikin harkar kasuwanci, ya fahimci yadda yanayin zai yi tasiri a rayuwar masu karamin karfi.
- 2023: ‘Hausawan Ebonyi’ sun goyi bayan dan takarar Gwamnan PDP
- Yadda CBN ya lashe amansa kan karbar tsoffin N500 da N1,000
Tinubu ya bayyana haka ne cikin sanarwar da ofishin watsa labaransa ya fitar mai dauke da sa hannun Abdulaziz Abdulaziz.
Da yake bayani yayin wata ganawa da ya yi da shugabannin ’yan kasuwa na kasa a Abuja, Tinubu ya ce a mastayinsa na wanda mahaifiyarsa ta ciyar ta kuma ilimantar da shi da kudin kasuwanci, yana iya fahimtar faduwa da kuma ribar ’yan kasuwa.
Don haka ya ce yana da masaniyar irin tasgaron da karancin kudi zai iya kawo a tattalin arziki na yau da kullum.
Ya nuna tausayinsa ga kananan ’yan kasuwa musamman ’yan kasuwar kayan gwari, inda ya ce su ne wdanda tsarin zai fi shafa.
Tinubu ya bada misali da wani mai sayar da karas da ya hanga a yayin yakin neman zabe da ya tafi a Jihar Gombe, wanda ke tsaye kan kayansa a cikin rana ba tare da ko mutum guda ya sayi kayan ba, yana mai cewa hakan ya faru ne saboda rashin kudi a hannun jama’a.
Dan takarar ya yi kira ga ’yan kasuwa da kada su bari matsalar canjin kudin ta tunzura su.
Ya ce idan har ya yi nasarar lashe zabensa, to zai kirkiri hanyar bayar da bashi mai sauki ga ’yan kasuwa tare da magance masatlolin da suka addabe su.
Ya tabbatar wa ’yan kasuwar cewa ya san inda ke yi musu kaikayi, kuma zai sosa musu a matsayinsa na wanda ya fito daga gidan kasuwanci.
Wakilan shugabannin ’yan kasuwar da suka yi jawabi ga mahalarta taron sun bada kyakkyawar shaida a kan dan takarar wanda suka kira a matsayin daya daga cikinsu.
Sun yi alkawarin bayar da kuri’u masu yawa domin nasarar Tinubu, wanda suka bayyana a matsayin wanda ya fi sauran ’yan takarar nagarta.