Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN), ta gargadi jam’iyyar APC mai mulki kan tsayar da Musulmi da Musulmi a matsayin ‘yan takarar Shugaban Kasa da Mataimaki a zaben 2023.
Shugaban kungiyar, Rabaran Samson Supo Ayokunle, ne ya yi wannan gargadin ranar Lahadi a coci domin bikin Ranar Dimokuradiyya ta 2022 a Abuja.
Ayokunle, wanda ya samu wakilcin Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya ta Pentecostal, Bishop Francis Wale Oke, ya ce hakan ba zai amfana wa Najeriya komai ba.
A cewarsa, kowane yanki na Najeriya da addini yana da kwararrun mutane da za su iya mulkin kasar nan.
Ya ce daidaito a tikitin takara tsakanin bangarorin biyu na addinai zai taimaka wajen rage zafin adawar siyasa, da samar da fahimtar juna da zaman tare.
“Yayin da muke taya wadanda suka yi nasara a zaben fid-da-gwani na Shugaban Kasa murna, muna rokonsu da su kula da bukatarmu. Yana da mahimmanci.
“Don Allah kar a gwada tikitin Musulmi da Musulmi; kamar ana kokarin kitsa rikici ne. Ba abu ne mai yiwuwa ba. Hakan zai haifar da rashin jituwa tsakanin al’ummomin Najeriya,” inji shi.
Sai dai ya yi kira ga miliyoyin Kiristoci a kowane bangare na kasar nan da su sani cewa ‘yan takarar da dukkanin jam’iyyun siyasa suka fitar na kowa da kowane, wato Musulmi da Kiristoci.