Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bukaci rushe kotunan shari’ar Musulunci nan take, a kafa kotunan addinin Kirista.
Shugaban CAN, Reshen Jihar Kano, Rabaran Adeolu Adeyemo, ya bukaci a soke duk tanade-tanaden da suka danganci kotunan Musulunci a Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, yana mai cewa Kiristocin kasar sun amince ta ci gaba da zama ’yar ba-ruwamnu da addini, kamar yadda Sashe na 10 na Kundin Tsarin Mulki ya tanada.
Shugaban na CAN ya kuma bukaci a tabbatar da adalci da daidaito a bangaren rabon gado tsakanin maza da mata da kuma ’yancinsu na samun ilimi da sauransu.
Ya bayyana hakan ne a Kano, a lokacin sauraron ra’ayoyin jama’a kan gyaran Kundin Tsarin Mulki da Kwamitin Majalisar Wakilai ya gudanar a Jihar Kano.
Rabaran Adeyemo ya ce idan kuma ba za a rushe kotunan Musulunci ba, to a gyara tsarin mulkin a samar da kotunan Ikilisiya (Kirista) domin yin adalci ga kowane bangare, tunda an riga an kafa kotunan Musulunci.
Idan har aka samar da Kotunan Ikilisiya, to za su rika amfani ne da dokokin addinin Kirista wajen gudanar da shari’a da yanke hukunci.
CAN ta kuma bukaci a rabe tsakanin ofishin Ministan Shari’a da na Antoni Janar na Tarayya, sannan a ba wa bangaren shari’a ’yancin cin gashin kai a bangaren kudi.
Tana kuma bukatar a magance batun bambanci tsakanin ’yan asali kasa da mazauna tare da samar da dokokin da za su tabbatar da hukunta masu karya dokar.
Sauran bukatun da CAN ta gabatar wa kwamitin wanda Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai, Alhasan Ado Doguwa, sun hada da samar wa sarakunan gargajiya da shugabannin addini matsayi a kundin tsarin mulki.