Hukumar Kwallon Kafar Afirka (CAF) ta ce za ta yi wa dan wasan Super Eagles na Najeriya, Victor Osimhen, gwajin amfani da kwayoyin da ke sanya karin kuzari.
Shirin yi wa dan wasan gwajin na zuwa ne bayan nasarar da Najeriya ta samu a kan Kamaru a wasansu na karshe a gasar cin kofin nahiyar (AFCON 2023) da ke gudana a Ivory Coast, inda Najeriya ta cire Kamarun a zagayen ’yan-16.
Victor Osimhen wanda shi ne Gwarzon Dan Wasan Afirka na 2023, ya kokarta sosai a karawar da suka doke Indomitable Lions na Kamaru da ci 2-0, wanda hakan ya ja hankalin hukumar CAF.
Rashin gajiyar dan wasan a karawar ne ya sanya CAF neman yi masa gwajin amfani da kwayoyin kara kuzari.
- An daure dan bindiga shekaru 21 a Kaduna
- Daliba ta kashe kanta saboda lakcara ya daina son ta a Adamawa
Osimhen ya yi ta zarya a wasan, inda har ya samu nasarar kwace kwallo a kafar mai tsaron bayan tawagar Kamaru, ya yi wa Ademola Lookman fasin, shi kuma ya zura a ragar Kamaru.
An ci gaba da wasan da Osimhen a matsayin barazana ga masu tsaron bayan Kamaru har zuwa lokacin da aka cire shi daga wasan.