✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

CAF za ta karrama Osimhen, Nwakali da Amunike A Abuja

Akalla ’yan kwallon Najeriya shida ne ake sa ran za su karbi kyaututtuka daban-daban daga Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) a ranar 7 ga…

Akalla ’yan kwallon Najeriya shida ne ake sa ran za su karbi kyaututtuka daban-daban daga Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) a ranar 7 ga watan Janairun 2016 a Abuja.  A ranar ce Hukumar CAF tare da hadin gwiwar Kamfanin Sadarwa na GLO za su karrama ’yan kwallon da suka yi fice daga Nahiyar Afirka, kuma a ranar ce za a zabi Gwarzon dan kwallon Afirka.
Bayanin haka na kunshe ne a wata sanarwa da Hukumar CAF ta fitar a ranar Litinin din da ta wuce.  ’Yan kwallon da Hukumar CAF din ta zakulo daga Najeriya da za a karrama sun hada da Emmanuel Amuneke, Kocin kungiyar kwallon kafa ta ’Yan kasa da Shekara 17 (U-17) da ya lashe Kofin Duniya na matasa a Chile kuma ana sa ran zai karbi kyautar kocin da ya fi kokari a Nahiyar Afirka a shekarar 2015 (Coach of the Year) sai bictor Osimhen da Kelechi Nwakali dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a gasar ’yan kasa da shekara 17  a Chile da kuma wanda ya fi nuna kwazo a gasar, wanda hukumar za ta ba su kyautar gwarazan matasan ’yan kwallo na shekara (Youths Player of the Year Award) sai Ngozi Ebere da za ta karbi kyautar Gwarzuwar ’Yar kwallon ta shekara a bangaren mata (Women Player of the Year Award).
Sauran sun hada da Azuibuike Okechukwu da Etebo Oghenekaro wadanda za a ba kyautar ’yan kwallon da ke tashe (Most Promising Talent Award).
Haka kuma hukumar ta fitar da sunayen ’yan kwallo uku da za su fafata a Gasar Gwarzon dan kwallon Afirka (African Football of the Year Award), kodayake babu dan Najeriya a cikinsu.
Sunayen ’yan kwallon uku da aka zakulo su ne Pierre-Emerick Aubameyang dan Gabon da ke buga wa kulob din Borussia Dortmund na Jamus kwallo, sai Yaya Toure, dan Kwaddebuwa da yake yi wa kulob din Manchester City na Ingila kwallo sai Andrew Ayew dan Ghana da ke yi wa kulob din Swansea na Ingila kwallo.