✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Caca na yi da kudin fansar karamar yarinya —Matashi

Wani matashi da ake zargi da garkuwa da wata karamar yarinya a Kano ya ce ya kashe kudin fansar da aka ba shi wurin aikata…

Wani matashi da ake zargi da garkuwa da wata karamar yarinya a Kano ya ce ya kashe kudin fansar da aka ba shi wurin aikata masha’a.

Matashin mai shekara 24 da ya nemi Naira miliyan 10 daga mahaifan yarinyar, ya ce ya yi caca, neman mata da shan kwayoyi ne da kudin.

“Dubu dari biyar na karba: na yi caca, na yi neman mata na yi shaye-shaye a Kaduna”, inji matashin da ya ce garinsu daya da yarinyar.

Da ake gabatar da shi, ya shaida wa Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano cewa shi ya sace yarinyar mai shekara takwas ya tsere da ita a kan babur.

Ya kara da cewa, “Da muka tafi hanya sai muka fadi a mashin ta mutu… na haka rami na binne ta”, amma duk da haka ya karbi kudin fansa daga wurin iyayenta ya kuma kashe.

Tuni dai jami’an Rundunar na Operation Kan Ka Ce Kwabo suka hako gawar marigayiyar suka mika wa mahaifinta.

A ranar 6 ga watan Nuwamba ne ’yan sanda suka damke matashin a Kaduna bayan kwana 154 suna hakon shi.

“Tun lokacin da mahaifinta ya kawo mana kara muke bin lamarin kuma daga Kano ya kai mu jihohin Jigawa, Katsina, Kaduna, Abuja da garin Aba a Jihar Abia kafin daga baya muka cafke shi”.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Kano, Haruna Kiyawa ya ce suna ci fadada bincike a kan wanda ake zargin kafin a gurfanar da shi a kotu.