Sojin da ke jagoranci a kasar Burkina Faso sun rattaba hannu kan yarjejeniyar mulkin shekaru uku gabanin damka ragamar mulki ga fararen hula wata guda bayan juyin mulkin kasar da ya hambarar da shugaba Roch Marc Christian Kabore.
Bayan doguwar tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki na Burkina Faso ciki har da kungiyoyin fararen hula da bangarorin tsaron kasar, da aka fara a ranar Litinin zuwa Talata ne aka tabbatar da matsayar ga manema labarai.
- FIFA ta dakatar da Rasha daga buga kofin duniya na 2022
- Ramadan: Sarkin Saudiyya zai ba ’yan Najeriya 12,600 abinci
Jagoran mulkin sojin na Burkina Faso Laftanal-Kanal Paul-Henri Sandaogo Damiba, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar mulkin wadda ta sahale masa jagoranci har nan da watanni 36 kafin Babban Zaben kasar.
Matakin na zuwa ne bayan taron majalisar tsaron kasar ya saba da kudirin farko na mulkin watanni 30 da sojojin suka gabatar kafin mayar da kasar turbar dimokuradiyya.
Taron ya kuma kunshi jam’iyyun siyasa da kungiyoyin matasa da na mata, sannan wakilcin daukacin mutanen da hare-haren ta’addancin ya raba da matsugunansu a sassan kasar tun daga 2015 zuwa yanzu.