Magoya bayan sabon juyin mulkin da sojoji suka yi a Burkina Faso sun kai hari a Ofishin Jakadancin Faransa a babban birnin kasar, Ouagadougou.
Jami’an tsaro sun harba hayaki mai sanya hawaye kan masu zanga-zangar a harabar Ofishin Jakadancin bayan sojoji sun yi juyin mulki na biyu a shekarar 2022 a kasar.
- Mutum 174 sun rasu, 180 sun jikkata a turmutsutsu a Indoensiya
- NNPC ya saye gidajen mai 380 da kamfanin Oando
Dubban maso zanga-zangar sun yi zargin jagoran gwamnatin sojin kasar da aka kifar ya boye a ofishin jakadancin domin dakile juyin mulkin da aka yi masa.
Mutanen sun banka wuta a zagayen katangar ofishin, suka rika jifa da duwatsu, lamarin da ya sa sojojin Faransa da suka ja daga a kan rufin ginin harba musu hayaki mai sanya hawaye.
A ranar Juma’a kasar Burkina Faso ta bude wani sabon babi a siyasarta inda wani karamin hafsan soji, Kyaftin Ibrahim Traore, ya sanar da hambarar da gwamnatin shugaban juyin mulkin farko, Paul-Henri Sandaogo Damiba, bisa zargin kasa murkushi mayaka masu ikirarin jihadi.
Juyin mulkin dai shi ne na biyu a kasa da shekarar guda a Burkina Faso da ke Sahel, yankin da yawancin kasashensa ke fama da mayaka masu ikirarin jihadi.
Sanarwar da sabon shugaban jin mulki, Ibrahim Traore, ya fiar ranar Asabar ya yi zargin Damiba “ya boye a sansanin Faransa da ke Kamboinsin domin kawo wa dakarunmu matsala”.
Daga baya a ranar Asabar Damiba a karyata zargin, amma bai iy karin haske ba bayanin nasa na farko tun bayan kifar da shi.
A sanarwar da ya fitar ta Facebook, Damiba ya yi kira da masu juyiyn mulkin da su “koma cikin hankalinsu kada su jefa kasar cikin yaki mara fa’ida”.
Shugaban Ma’aikatan sojin kasar Burkina Faso dai ya ce ba juyin mulki aka yi ba, rikicin cikin gida sojojin suka samu kuma ana tattaunawa domin samun maslaha.
A ranar 16 ga waan Janaiur, 2022 ne dai Damiba ya hau mulki bayan ya yi wa gwamnatin Roch Marc Christian Kabore bisa zargin rashin murkushe mayakan jihadi.
A ranar Asabar din dai, Faransa, wadda a baya ta i wa Burkina Faso mulkin mallaka ta nesanta kana da juyin mulkin, ko karbar bakuncin wani jami’in gwamnatin kasar..