✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina shi ne in zama kwararren mai hada hotunan bidiyo da siddabaru – Abubakar Sadik

Mene ne takaitaccen tarihinka? Sunana Abubakar Sadik Muhammad, an haife ni a Layin Jama’a a garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a. Na yi makarantar…

Mene ne takaitaccen tarihinka?

Sunana Abubakar Sadik Muhammad, an haife ni a Layin Jama’a a garin Kafanchan da ke karamar Hukumar Jama’a. Na yi makarantar firamare a Ahmed Makarfi National Schools kuma yanzu haka ina ajin karshe a makarantar Sakandare ta National College kuma ni ne Shugaban dalibai (Head Boy).

Mene ne takamaiman abin da kake yi?

Ina harkar gyara hotuna ne da bidiyo. Kuma na fara wannan harkar ce da na hotuna tun ina aji shida a firamare. Ina yin amfani da wayar hannu ne da kuma kwamfuta. Idan na dauki bidiyo dan kadan misali sai in shiga in fara hade-hade a cikin Intanet. Nakan dauki bidiyon gutsi-gutsi ne sai in zo in harhada har na fara saka fassara (Subtitle). Da kadan-kadan da na fahimci Allah Ya ba ni baiwar aikin sai na fara tunanin yadda zan bunkasa harkar, hakan ya sa nake shiga cikin kamfanoni da ma’adanan da suka jibinci irin wannan sana’a a Intanet ina sayen manhajoji na siddabaru ina gwadawa har ga shi yanzu cikin ikon Allah, duk da dai da saurana tunda ba abu ne da ake gama iya shi ba, amma dai a yanzu babu irin bidiyo na fim ko na mawaki da ba zan iya hada shi in kuma saka abubuwan da ake bukatar sakawa ko da na siddabaru ne kuwa ba.

Ya zuwa yanzu ka yi aiki a wasu fina-finai na bidiyo?

Da yake yanzu nake tasowa kuma mutane ba su san ni ba tukuna, amma dai akwai wasu ayyuka na biki da na yi sai kuma na wasu mawaka da muke da su a nan garin Kafanchan.

Wane aiki ne ka yi wanda ya fi burge ka har kake jin kana da nasibi a wannan harka?

Ka ga na farko zan iya hada maka hadari tare da walkiya har zuwa zuban ruwan sama. Amma aikin da na yi a wani shiri ne na wani fada da wadansu mutum biyu suka gwabza. Shi wannan fadan wani mafarauci ne da yake jin kansa da tsafi, sai fada ya hada shi da wani Bafulatani, to a lokacin da za su fara sai wannan mutumin ya bace. bacewarsa ke da wuya sai Bafulatanin ya bugi kasa da hannunsa sai kasar ta tsage sai ya bi wannan mafaraucin karkashin kasa suka ci gaba da fada, kasa na girgiza kuma ana jin kara a karkashin kasa. Duk wadannan abubuwan za ka gan su a zahiri tun daga bacewar zuwa girgizar kasar da shigewa cikinta da karar fadan a karkashin kasa tana motsawa. Ina alfahari da wannan kwarewar da nake samu duk da ban fara yin wasu ayyuka da aka san ni ba tukuna. Burina shi ne a duk lokacin da na kammala makaranta in shiga aikin gadan-gadan. Shi ya sa nake ajiye ayyukan da nake yi don in rika sanin ta inda na faro da kuma abubuwan da zan kara nemowa kuma su zan rika nuna wa duk wanda yake son ganin aikina.

Zuwa yanzu ka yi ayyuka kamar nawa?

Tsakanin ayyukan gwaji da na biki da kuma na kananan mawakan da muke da su sun haura goma.

Mene ne burinka nan gaba kan wannan aiki?

Burina shi ne idan na kammala makaranta in kama aikin gadan-gadan inda zan yi amfani da shi in sake karo ilimi sannan a karshe fatana in zamo wanda duniya za ta jinjina masa. Ina so in samu manyan kayan aiki nan gaba kuma in shahara a san ni a duniya kan ayyukan siddabaru da sauransu ta fuskar tace fina-finai.

Akwai wasu ayyuka da kake yi ne bayan wannan?

Eh, ina aikin kafinta kuma ina sayar da gwanjo. Sannan ana kawo min hoto in gyara in saka irin abubuwan da mutum ke so a ciki in tura wa mutum a wayarsa kamar  hotunan ’yan takara da ke yin kamfen da su a kafafen sada zumunta na zamani.

Yaya batun matsaloli ko akasin haka?

Alhamdulillah zuwa yanzu dai babu wata matsala da na fara fuskanta. Batun alheri kuwa idan na yi wa wasu aiki ko na biki ko mawaka ina dan samun wani abu a wajensu kuma da sannu a hankali an fara sanina.