Hajiya Ubaida Bello, hazika ce da ta samu gagarumar nasara a rayuwa. Ita ce mace ta farko da ta shahara wajen taimakon marasa galihu musamman marayu a Jihar Sakkwato. Hakan ya sa kungiyoyin taimakon al’umma da ke sassan duniya suka hada kai da ita wajen tallafawa al’umma musamman a Jihar Sakkwato. Tun bayan da ta kammala karatu ba ta yi aikin gwamnati ba amma ta kafa kungiyar sa-kai na kashin kanta mai suna Hikma Komdi (HCKOMDI) da ke tallafawa al’umma ta fuskoki da dama. Wakilinmu ya yi hira da ita inda ya ji irin fadi-tashin da ta sha da nasarorin da ta samu da sauran batutuwa da dama game da rayuwarta kamar haka:
Asalinta da Ayyukkanta:
An haife ni ne a Unguwar Hungumawa dake cikin garin Sakkwato a karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa. Na yi karatun firamere a makaratar Waziri inda na kammala a 1988. Daga nan na yi Sakandare a Kwalejin ’yan mata ta Gwamnati da ke Sakkwato daga 1989 zuwa 1994. Bayan dogon hutu da na yi sai na cigaba da yin karatu a Jami’ar Usman dan fodiyo inda na kammala 2011 a bangaren ilimin jikin dan Adam (Biology).
Na tsunduma cikin ayyukkan sa kai gadan-gadan don ceto al’ummata musamman masu karamin karfi inda na yi aiki a kungiyoyin sakai daban-daban kiamar haka: Yanzu haka ina aiki da wata kungiyar sa-kai mai suna Serbice Delibery Specialist (USAID/PLAN/LEAD) Sakkwato. kungiya ce da ke kokarin samar da cigaba ga mutane. A shekarar 2014 ce na zama Jami’ar sadarwa ga al’umma a kungiyar sa-kai ta COMMUNAID/AMSAG DEbELOPMENT CONSULTING NIGERIA. Na kuma zama mataimakiyar mai bincike ta British Council, Nigeria da EDOREN/UNICEF da BBC WORLD amma tun a shekarar 2010 ne na yi aiki tare da su, Sannan na zama memba a kungiyar mata ta Jihar Sakkwato kuma jami’ar kula da yadda ake kashe kudi a gamayyar kungiyoyin sa kai na jiha daga 2010 zuwa 2016. Memba a makaratar almajirai ta kasa dake Gagi. Memba a firamaren Hungumawa. Mamba a kungiyar sa kai ta Iron Ladies Debelopment Initiatibe (ILDI). Sammam ni ce Shugabar Hikima Komdi, kungiyar sa- kai da taimakon al’umma a tsakanin shekarar 2013 zuwa2014. Mataimakiya a shirin ObC a 2011 zuwa2013, ‘Yar takarar kujerar majalisar dokokin Jihar Sakkwato a shekarar 2011. Sakatariya ga masu aikin cutar cizon sauro da tamowa da allurar shan inna a shekarar 2008. Mataikaiyar ko-odineta a kungiyar matasa ta kasa kan ciwon sida 2004 zuwa 2008. Mataimakiyar Sakatare- Janar ta hadakar kungiyoyin sa kai na Sakkwato 2005 zuwa2009. jami’ar koyar da shirin manyan mata 2004 zuwa2010. Na yi kwasa-kwasai da dama irinsu na TSHIP da NEI/USAID da EU da SOSACAT da ICT Sakkwato, da saurnsu.
Taron karawa juna sani:
Taron kasa kan kayan sadarwa irin na zamani da gwamnati a Cibiyar Taro na Shehu Musa ‘yar Aduwa da ke Abuja. Da taro kan sanin yadda harkokin gwamnati ke tafiya da aka yi a Kaduna, da wani taro kan kara wa juna sani a 2006. Makarantu da siyasar mata a Afirika wanda Jami’ar danfodiyo da Jami’ar Balin ta kasar Jamus suka gudanar. Gudunmuwar kungiyoyin sa kai don habaka siyasar mata da wakilcinsu wanda UNDP suka shirya. Da kuma wani taro kan shirya kasafi a tsakanin kananan hukumomi da na jiha. Da taro kan hada kai tsakanin majalisar zartarwa da ta dokoki kan bukatun al’umma, dukkan wadannan tarurruka Hukumar UNDP ce ta shirya. Da sauran tarurrukan da na halarta da dama wadanda ba zan iya jero su a wannan lokaci ba daga cikin 22 da na halarta a nan gida da kuma a kasashen waje.
Nasarorinta:
Na samu nasarori da dama musamman na sauke Alku’arni tun ina da shekara 7. Na kammala digirina na danfodiyo a sashen halittar dan Adam (Biology) inda na samu kyakkyawan sakamako. Allah Ya albarkace ni da kafa kungiyar sa- kai tawa ta kaina mai suna Hikima Komdi (HCOMDI). Yanzu haka ina da ma’aikatan da yawansu ya kai 23 wadanda nake biyansu albashi duk wata. Haka kuma muna da ma’aikata na wucin-gadi (casual) da su ma muke ba su na-goro a duk wata.
Kukan samu kudin tafiyar da aikinmu ne daga kungiyoyin sa-kai daban-daban na duniya. Kawo yanzu mun tallafawa akalla marasa galihu da marayu su kimanin dubu 4. A cikin garin Sakkwato kimanin mutum goma ne muka daukewa sha’anin karatunsu. Mun zakulo yara mata marayu 20 da muke tallafawa ga karatunsu, duk wani abu da karatun ke bukata mun dauke tare da ba su kudin kashewa. Manyan mata dubu 1200 muke daukar nauyinsu ta hanyar koya musu sana’o’in hannu. Cutar sida (HIb) da mutane ke gudun masu ita mun rungumi masu dauke da cutar su kimanin 1,600 inda muke kula da su kuma muna ba su shawarwarin da suka dace don su cigaba da gudanar da rayuwa mai inganci.
Kalubalenta:
Na fuskanci matsaloli a rayuwata. Na daya a lokacin da mahaifina ya sanya ni a karatun boko an rika kallona tare da shi a matsayin kafirai wadanda suka kauce hanya. Haka muka dage har sai da na yi karatun. A lokacin da na kammala jami’a na samu matsalar rashin karbar sakamakona bayan share shekara shida ina karatun. Na so daukar matakin shari’a aka nuna min kada in yi hakan. Ban yi kasa a guiwa ba na koma karatun kasa gaba daya har na kammala. A matsayina na mace na samu barazana ganin duk abin da na ce zan yi sai na sha wahala kafin na samu nasara. Rashin sakewa da walwala sun yi mini tarnaki. Matar aure ce ni,
mijina muna kyakyawar hulda da shi. Yana taimakona da karfafa mini gwiwa. Ya kafa min kungiyata har yake ce min duk wanda ba ya harkar taimakon al’umma ba zai san halin da suke ciki ba. Yanzu ma ya wuce ni a harkar taimako. Gaskiya akwai kalubale don akwai abubuwan da nake son in yi masa amma wannan aikin ya hana. Ga kula da iyali sannan ga aiki, ga tafiye-tafiye, duk wadannan abubuwa sun zama kalubale a gare ni. Amma dai Alhamdulillah, komai yana tafiya cikin tsari da yardar Allah.
Wadda take koyi da ita:
Nana Khadija, matar Manzon Allah Annabi Muhammad (SAW) kan gudunmuwarta ga addini da tsayin dakanta ga kasuwanci. Da Nana A’isha wacce ta koyar da duniya ilmin addini, tana cikin mafi ruwaito hadisai. Ashe mata na da rawar da suke iya takawa. Da Nana Asma’u diyar danfodiyo da Sarauniya Amina Zazzau.
Tunawa da ita:
Ina son a rika tunawa da ni a matsayin mace wacce ta yi ilikmin boko da na addini wacce kuma tarbiyyarta ba ta gurbace ba. Sannan ina son a rika tunawa da ni a matsayin mace adila wacce ba ta son komai face taimakon al’umma musamman marasa galihu da marayu. Duk wani mai matsala ko wanda aka ha’inta nakan tsaya masa don ya samu hakkinsa.
Mata a harkar ilmi:
Matan Sakkwato muna da ilmi da fahimta. Shawarata ga mata ita ce su dage wajen neman ilimin addini da na boko. Sannan su kasance masu tarbiyya ga mazajensu. Haka kuma ina shawartar gwamnati da su rika ba mata mukamai don su ma a rika damawa da su a harkar gwamnati.