Hajiya Zainab Adamu Julde, Sarauniyar Sudan ta Akko, kwararriyar malamar makaranta ce kuma ’yar kasuwa. Ta yi gwagwarmayar rayuwa har ta zama Kwamishinar Harkokin Mata ta Jihar Gombe. A zantawarta da Aminiya ta bayyana irin gwagwarmayar rayuwa da ta yi kamar haka:
Tarihin rayuwata:
Sunana Hajiya Zainab Adamu Julde, ni Bafulatana ce kuma Batangaliya domin mahaifiyata Batangaliya ce, mahaifina kuma Bafulatani kuma an haife ni ne a garin Kumo, hedkwatar Karamar Hukumar Akko a Jihar Gombe. A can na girma iyayena suka sa ni a firamare ta Central da ke Kumo. Bayan na gama sai na tafi Sakandaren Arabiyya ta Mata da ke garin Alkaleri a Jihar Bauci wato Women Arabic Teachers Collage wacce yanzu ta zama Gobernment Girls Arabic Secondary School. Ina gamawa sai aka yi mini aure a 1989. Bayan nan sai na tafi Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Tarayya da ke Bauchi, inda na karanta diploma a fannin kasuwanci a tsakanin shekarar 2006 zuwa 2008, daga nan sai na tafi jami’ar nan ta karatu daga gida (Open Unibersity, NOUN) na karanta fannin sulhu da magance rikice-rikice (Peace and Conflicts Resolution) a tsangayarsu da ke Bauchi.
Aiki:
Na fara aikin koyarwa ne a Makarantar Firamare ta Central da ke Kumo bayan wani lokaci sai na koma Hukumar Tattara Kudin Shiga (Board of Internal Rebenue) da ke Kano, ina nan bayan wani lokaci sai aka mayar da ni sashen kula da harkar lafiya matakin farko na Karamar Hukumar Fagge a Jihar Kano, (Primary Health Care Department), a nan ne na ajiye aiki na ci gaba da harkokin kasuwanci gadan-gadan. Da ma lokacin da nake aiki ina kasuwanci na bude gidan sayar da abinci, mai suna Dadin-Kowa Restaurant a garin Bauchi ina kula da gidan abincina ne sai Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo ya dauko ni ya ba ni Kwamishinar Harkokin Mata a watan Janairu na wannan shekarar, amma kafin a ba ni Kwamishinar Mata na rike mukamin P.A mai taimaka wa Gwamnan kana daga bisani ya mayar da ni SSA (Senior Special Assistant) wato babbar mai taimaka wa Gwamna ta musamman.
Kwasa-kwasai:
Na yi kwas din Difloma a bangaren kwamfuta. Na yi kwas kan warware matsalolin tashe-tashen hankula, watoTrauma healing a Jos.
Nasara:
Na samu nasara sosai domin a dalilin kasuwancina da kuma aikin gwamnatin da nake yi, inda nake iya ciyar da jama’a har ma da ’yan uwa gaba a bangarorin rayuwa daban daban. Alhamdulillah, babbar nasarar ma ita ce gidan abincina da yanzu haka nake da ma’aikata kimanin hamsin da suke aiki a wajen.
Kalubale:
Mata har kullum suna fuskantar kalubale musamman wajen hada aikin gida da na ofis, ga kula da maigida da sauran dawainiya a wajen aiki kuma duk kokarin mace wadansu maza ba su so a ce mace ta yi kwazo alhali suna wajen.
Burina a rayuwa:
Burina shi ne in ga ina taimaka wa ’yan uwana mata ta bangaren karatu da kiwon lafiya musamman wadanda suke karkara da ba su da karfi.
Tufafin da ya fi burge ni:
Na fi son in daura atamfa zane da riga sannan in yafa gyale, in yi fita irin ta mutunci, kowa ya gan ni ya ga fita ta kamala da kamun kai.
Hutu:
Ba na zuwa hutu ko’ina, a lokacin hutu ina yin sa ne a tsakanin iyalina daga garin Kumo zuwa Gombe zuwa Bauchi.
Kungiyoyi da kasashe:
Ni mamba ce a Kungiyar Kwararru a Harkar Shugabanci (National Institute of Management NIM), sannan Shugabar kungiyar Mata a Harkokin shugabanci wato Women in Leadership.
Kasashen da na ziyarta sun hada da Saudiyya da Indiya da Dubai da sauransu.
Yawan iyali:
Alhamdulillah ina da ’ya’ya hudu, mata uku, namiji daya.
Shawara ga iyaye:
A matsayina ta uwa ina bai wa iyaye shawarar idan sun gane karatun ’ya mace abin yi ne. Idan ta yi karatu ko wajen zaman gidan aurenta zai bambanta da na wacce ba ta yi ilimi ba. Idan aka ba mata ilimin addini da na zamani rayuwarsu za ta inganta matuka. Sannan ba na goyon bayan yi wa yarinya auren wuri a hana ta karatu ko da sakandare ne balle kuma masu dora wa ’ya’yansu talla irin wadannan iyayen kamar sun bai wa ’ya’yan lasisi ne na lalacewa.