Malama Halima Idris tsohuwar malamar makaranta ce da ta dade tana karantarwa a makarantu masu zaman kansu da dama. A yanzu baya ga karantarwar, ita ce mai lura da Makarantar Nursery da Firamare mai zaman kanta mai suna Ahmed Makarfi National Schools da ke garin Kafanchan, hedkwatar karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna. A wannan tattaunawar da ta yi da Aminiya ta bayyana tarihin rayuwarta tare da irin kalubalen da ta fuskanta da kuma shawarwarin da za a bi don inganta harkar koyarwa a matakin farko, wato makarantun Nursery da kuma Sakandare, da ma sauran bayanai.
Aminiya: Ki fara da ba mu tarihinki a takaice?
Sunana Halima Idris. An haife ni a cikin garin Kafanchan a shekarar 1978. Sai dai a zahirin gaskiya ban girma a gaban iyaye na ko a mahaifana ba domin na taso ne a garin Legas daga nan kuma muka dawo Kano da zama.
Na fara karatun firamare ne a Army Children’s School da ke Dodan Barrack da ke Legas daga nan lokacin da Babana zai tafi aikin Haji kuma ya ga tafiyar zai ban wahala saboda nisan inda muke sai aka dawo da ni Nigerian Air Force Primary School duk dai a Legas din inda na kammala firamare na nan. Daga nan na shiga Kwalein ‘Yan Mata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) da ke garin Onitsha cikin Jihar Anambra inda na kammala karatun sakandare sannan na je na yi karatun Difiloma a fannin ilmin kwamfuta.
Bayan mun dawo Kano sai na fara dan sarin kayayyaki haka ina sayarwa har zuwa lokacin da na yi aure ban bar neman na kaina ba. Abin da ya kama daga saka da kuma saye da sayarwa duka ina tabawa saboda mu taru mu rufa wa juna asiri. A yanzu haka ni malama ce a makarantar Ahmed Makarfi National Schools da ke garin Kafanchan.
Aminiya: Daga wanne lokaci kika shiga harkar koyarwa?
Na fara koyarwa ne a shekarar 1994 a makarantar Ilmi Comprehensibe School da ke Kafanchan sai dai makarantar ta zo ta tsaya bayan rikicin Kafanchan da aka yi na shekarar 1999. Daga nan ne kuma a shekarar 2004 na fara koyarwa a Ahmed Makarfi National Schools (da ya kunshi sashen Nursery da Firamari da kuma Sakandare) a nan Kafanchan inda nake ci gaba da koyarwa da kuma lura da makarantar har zuwa yanzu.
Aminiya: Da ma me kike sha’awar zama a lokacin tasowarki?
Babban abinda na ke sha’awar zama a sadda nake karama shine ma’aikaciyar lafiya (Nurse) sai dai Allah bai nufi hakan ba saboda sau da yawa kana naka ne Allah yana naSa. Yanzu ni babban aikin da nake sha’awa shi ne samun wasu kungiyoyi wadanda suke fafutukar kare hakkin yara da mata domin yin aiki tare da su. Ina sha’awar zamowa daya daga cikin wadanda za su rika tallafa wa kananan yara marasa galihu da kuma kwatowa yara da mata hakkokinsu idan an danne.
Aminiya: A matsayinki na malamar makaranta ko za ki fada mana kadan daga cikin halin da makarantun firamare da sakandare suke ciki a halin yanzu kuma ta yaya ki ke ganin za a iya shawo kansu?
Ka ga duk aikin da na yi a makarantu ne masu zaman kansu. Amma idan mun koma kamar bangaren makarantun gwamnati za ka ga suna fama da matsaloli na ko dai matsalar rashin isassu ko kwararrun malamai ko kuma rashin tsayawa kai da fata ko kuma ka ga mutum ga shi yana da kwalin amma abin takaicin wani sai ka ga hada bakake ma ya karanta ya zama masa matsala. Dole gwamnati ta sanya ido sosai a makarantunta na firamare da kuma sakandare domin su ne tushen duk wani karatu da mutum zai yi a rayuwa.
Wadannan kadan ne daga cikin irin matsalolin da makarantun yanzu ke fuskanta wanda in har ana so a shawo kansu to dole gwamnati ta kula da yadda ake karantar da yara.
Zan ba ka misali da inda nake aiki. Ka ga makaranta ce ta kudi to shi shugaban makarantar akwai abin da yake yi kulli yaumin da zai sa dole malami ma ya shiga taitayinsa domin kana zaune kawai za ka ga mai makarantar yazo ya dudduba duk abinda ya san ya kamata ayi ya kuma duba me da me aka koyar da yara a lokuta kaza da sauransu. Idan har ya gama dubawa aka kuma samu matsalar da mutum ya san cewa wannan sakacinsa ne to akwai hukuncin da yake mana ka ga hakan dole ta sa malami ya yi kokari don kar ya gamu da fushin mai makarantar tun da ya dauke ka aiki ne yana biyanka don ka yi masa aikin da ya sa ka.
Ka da malami ya damu da ko nawa ake biyansa amma ya duba irin alfanun ilmin da yake bayarwa wanda ba ma shi ko ’ya’yansa ba hatta jikokinsa za su amfana da shi.
Aminiya: Yaya batun hada aiki da kuma aikace-aikacen gida da tarbiyyar yara?
Gaskiya akwai kalubale kam, amma ni ka ga a lokacin da muka dawo makaranta to a lokacin kusan nake duk wasu aikace-aikace na girki da sauransu. Batun tarbiyyar yara kuma gaskiya muna iya kokarinmu domin aikin karantarwa ba aiki ne da zai iya takura ka ko ya hana ka lokacinka da za ka lura da yara ba don ba aiki ne irin wanda in ka je ofis tun safe sai misalin karfe shida za ka dawo ba ballantana ya zama ba ka da lokacin iyalinka ba, tana nan muna kokari sosai kuma muna samun lokacin lura da zirga-zirgar yaranmu da duk inda za su je, Alhamdulillah.
Aminiya: Yaya aka yi kika hadu da maigidanki har kuka yi aure?
Gaskiya wannan hadin iyaye ne domin mahaifina ya hada ni da shi ne tun ina karama saboda cika alkawarin da ya dauka. A lokacin ma ina makaranta in aka samu hutu sai in dawo dakin mijina in aka koma sai in koma makaranta.
Aminiya: Wacce nasihar mahaifiya ce ba za ki taba mancewa da ita ba?
Na fada maka tun farko cewa ba a gaban iyayena na girma ba sai dai a gaban iyayen goyo. To ita uwar goyona a kullum nasihar da take yi mini shi ne in zama mai hakuri a rayuwa haka ma idan na yi aure in zama mai hakuri da
zamantakewar aure kada in zama fitinanniya mai takurawa miji kan lallai sai ya kawo abin da ba shi da shi. Ta kan mini nasiha in zamo mai kulawa tare da girmama mutane ko da ko na kasa da ni ne don ban san irin baiwar da Allah Ya yi masa ba kuma Alhamdulillahi har yanzu ina ganin amfanin wadannan nasihohin.
Aminiya: Wacce mace ce ki ke koyi da ita a rayuwa?
Ina koyi ne da duk macen da a duk lokacin da na dauki kuka na na kai musu su kan ce da ni na ci gaba da yin hakuri domin zan ci ribar rayuwa.
Aminiya: Mene ne burinki a rayuwa kuma da me ki ke so a rika tunawa da ke?
Ina so wannan karantarwar da nake yi a rika tuna ni da ita ko bayan raina. Kuma burina in ga na kwato wa yara da mata hakki.
Aminiya: Wanne irin abinci kika fi so?
Na fi son shinkafa Jolof. Ta bangaren abincin gargajiya kuma na fi son fate
Aminiya: Tufafin da kika fi sha’awa fa?
Zani da riga da duk wani kaya na mutunci.
Aminiya: Ya batun iyali?
’Ya’yana shida ne kuma dukansu sun kammala makarantar sakandare. daya na shirye-shiryen zuwa makarantar aikin jinya (School of Health Technology) daya kuma zuwa Kwalejin ilmi (College of Education).
Aminiya: Mece ce shawararki ga iyaye mata game da ilmin ‘ya’ya mata a wannan zamanin?
Ka san an ce idan ka ilmantar ko ka tarbiyyantar da diya mace kamar ka ilmantar da al’umma ne don haka ina kira ga iyaye mata da su zage damtse wajen ilmantar da ‘ya’yansu da lura da tarbiyyarsu. Sannan mu rika lura da duk makarantun da suke zuwa neman ilmi da kuma irin kawayen da suke abota da su. Wani lokaci sai ka ga yakamata a ce yara na gida don ba lokacin makaranta ba ne amma sai ka ga iyayen ba su damu ba to hakan zai iya haifar da matsala kafin mutum ya farga, Allah ya kiyaye.