✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Burina in ga ana damawa da mata a harkokin siyasa – Hajiya Salamatu Isah Abdullahi

Tarihinta: Sunana Salamatu Isah Abdullahi. Ni haifaffar Jihar Sakkwato ce.  Iyayena sun fito ne daga karamar Hukumar Yabo. Na yi firamare a garin Zuru amma…

Tarihinta:

Sunana Salamatu Isah Abdullahi. Ni haifaffar Jihar Sakkwato ce.  Iyayena sun fito ne daga karamar Hukumar Yabo. Na yi firamare a garin Zuru amma na kammala a Argungu, saboda mahaifina ma’aikacin gwamnati ne a lokacin.  Daga nan aka mayar da ni sabuwar sakadaren mata ta garin Jabo, ba a gina makaratar ba sai aka kawo mu wucin-gadi a Kwalejin ’Yan mata ta Sakkwato (GGC), bayan shekara daya aka mayar da mu Jabo. Bayan sojoji sun karbi mulki ne aka rusa ta aka mayar da mu Tambuwal gaba daya. A can na kare sai dai jarrabawa ba ta yi kyau ba sai na koma gyara na rubuta JAMB domin ina da burin kafin a yi min aure in shiga jami’a.  Kan haka na fara karatun share-fagen shiga jami’a, ina karatun ne aka yi mini aure sai karatun ya tsaya, daga baya na ci gaba, na kammala digirina a fannin shari’a a Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato.

kalubalen da ta ci karo da su a rayuwa:

Ba za a rasa ba, musamman karatu domin a lokacin karatu da aure yana da wuya, yanzu kam alhamdulillah komai ya wuce, mun samu gagarumar nasara a rayuwa don ina cikin wadata daidai gwargwado sai godiyar Allah.

Abin da ya faru da ita da ba za ta taba mantawa da shi ba:

Gaskiya babban abin da ya same ni da ba zan taba mantawa da shi ba shi ne, rashin kare karatu tare da abokan karatuna, don a lokacin mai gidana ba ya da lafiya, ga ni da yaro da nake shayarwa shi ma a kwance a asibiti ba lafiya. Haka na yi ta wannan dawainiya abin da ya zame mini karfen kafa a lokacin, amma dai ga shi ya wuce duk da ba zan manta da shi ba. 

Abin da take son a tunata da shi bayanta:

Abin da nake son a tuna ni da shi bai fi wannan gwagwarmaya ta siyasa ba, ta ganin mata sun fito sun shiga zabe an taka rawa da su, sun zaba, an zabe su, a sauya wannan tsari na su tura mota a bar su da hayaki. Yadda maza ke shiga karatu haka mata ke yi. Ai mata shugabanci ne kadai ba mu yi amma muna wakilci.  Ina son a rika tuna ni a matsayin wacce ta yi  tsayin- daka wajen ganin mata sun fito sun shiga takara a zabe a kan duk wata kujera tun daga matakin kansila har zuwa ta dan Majalisar Tarayya. Wadannan abubuwa sun sanya ni shiga gwagwarmaya ta siyasa. Abin takaici ne yadda mata suke bayar da gudunmawa a harkar siyasa amma sai ka tarar mukamin da ake ba su bai wuce daya ko biyu ba.  

Yadda take kallon mata a  siyasar Najeriya:

A kasa baki daya, mata sun samu damar taka rawar gani a wasu jihohi inda akwai macen da ta yi takarar Gwamna. Amma a nan Sakkwato fitowar mata a siyasa ya yi karanci watakila saboda dalilan addini ko danniya ta maza da suke hada addini don su danne mata, domin duk abin da ake yi na neman jama’a da cin zabe da matan ake yin sa, su mata ba su iya siyasar banga da ubangida da taron tsakar dare ba, wadannan matsaloli mata na fuskantarsu bayan ba su dama a fafata da su da aka ki yi. Tsarin bai wa mata mukami na gwamnatin Sakkwato karkashin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal shi ma ban gamsu da shi ba. Bai dace a ce kwamishina biyu da  mashawarta biyu kadai za a ba mu ba, tunda duk wahalar kafa gwamnati da mata aka yi ta. Ya kamata a bai wa mata dama da yawa a sanya su a wurare da dama, a daina maimaita matan da ake bai wa mukami kuma a fadada abin, tunda akwai matan da ya kamata su ba da ta su gudunmawa fiye da wadanda ake ba yanzu. A bude lamarin domin taimakon da gwamnati ke bayarwa ga tallafa wa mata da kananan yara ya iya shiga hannunsu kan haka za ka iya cewa ba wani tallafi na a-zo-a-gani da gwamnati ta bai wa mata.  Kullum in ka ji an taimakawa mata cibiya ce ta koyon sana’a aka bude musu.  Ya kamata a ce mun wuce wannan. A karfafa mata su iya fitowa a yi gwagwarmaya da su, a sanya su cikin tsarin gwamnati, su fito da baiwar da Allah Ya ba su. Duk da mun kasa gane alkiblar gwamnatin nan, kowa sai kuka yake yi da ita, idan ta bullo da wani shiri, kafin a fara sai kuma a sake rushewa a dauko wani.  Ya kamata gwamnatin ta mayar da hankalinta waje daya.

Burinta ya cika: 

Burina ya cika domin ba ni da wata bukata kamar mutanenmu sun yarda mata ’yan siyasa, mutane ne masu mutunci kamar yadda na shigo mutuncina bai taba zubewa ba. Da wannan nake cewa burina ya cika, kuma ina so matan kasar nan su shiga zabubbuka a kasar nan, ba wata tsangwama da kyara.

Yaya take kallon tarbiyyar ’yan mata a yau:

To abin kam sai addu’a sai dai Allah Ya kawo sauki. Sakacin iyaye da hukuma ne ya lalata tarbiyyar mata a yanzu, musamman shaye-shayen da suka rungumasun tsunduma su cikin kwadayin abin duniya da rashin kunya. 

Shawararta ga mata:

Shawara ta gare su ita ce su dage ga aikata abin da zai taimake su, duk inda za su shiga su san su mata ne, komai su zama suna tsare mutuncinsu. Mata rayuwarmu ragagga ce don haka mu daina sake muna sanya kanmu cikin halaka da da-na-sani, komai mu rika yin sa bisa karantarwar addinimu. Mu daina kwaikwayon wadansu da ba jinsinmu daya da su ba. A duk inda muke, mu san akwai addinin da yake gadinmu da duk rayuwarmu.