Malam Abdullahi Aliyu Katsina shi ne shugaban kungiyar Awarness for Good Leadership, Peace and Debelopment (AGLPD) wato kungiyar Wayar da Kai kan Kyakkyawan Shugabanci, Zaman Lafiya da Ci Gaban kasa. a tattaunawarsa da Aminiya a ofishinmu ya bayyana dalilin kafa kungiyar da irin ayyukan da ta sanya a gaba:
Aminiya: Mece ce manufar kafa kungiyarku kuma mene ne burinta?
Manufar kafa wannan kungiya shi ne domin ta ilimantar da al’umma kan kyakkyawan shugabanci da samar da zaman lafiya domin sai dai su ne za a samu ci gaban kasa. Mun kafa kungiyar ce a shekara ta 2004, kuma yanzu haka muna da rassa a jihohi 18 na kasar nan Kudu da Arewa. Kuma muna gudanar da wannan aiki ne ta hanyoyi uku, shirya bita da buga kasidu da kuma fadakarwa ta kafofin watsa labarai. Yanzu haka mun shirya bita a jihohi da suka hada da Katsina da Zamfara da Kaduna da Kogi da kuma nan Abuja.
Dalilin da ya sa muka kafa wannan kungiya shi ne a baya na taba shiga siyasa, na shugabanci jam’iyya a matakin karamar hukuma, kuma na zama jami’in tattara sakamakon zabe a zaben Gwamnan Jihar Katsina a 1999, kuma na yi takara a nan Abuja. A wannan gwagwarmaya na fahimci mutane suna bukatar abubuwa biyu: Samun shugabanci nagari da ilimantar da al’umma kan wani tsari da ya dace da ita. Misali idan aka samu shugaba nagari kudirinsa da ayyukan da ya sanya a gaba za su sa jama’a su san suna da shugaba, saboda zai ba su hakkokinsu da suka rataya a kansu. rasa shugabanni nagari ne ke jawo matsalolin zamantakewa kamar rashin tsaro da tabarbarewar harkokin mulki da almundahana da sauransu. su kuma talakawa wadanda dole su ci abinci dole su tura ’ya’yansu makaranta kuma dole su rayu, tilas su bullo da hanyoyin cimma hakan komai muninsu. To rashin shugabanci nagari ya haifar da cin hanci da rashawa da kabilanci shi ya sa aka rasa inda aka sanya gaba a kasar nan. Sannan ba a ilimantar da jama’ar kasa cewa babu wata kasa da za ta ci gaba ba tare ana ilimantar da jama’arta kan al’amuran da suka shafi gwamnati da rayuwarsu da makomarsu ba. Wannan ya sa yanzu haka muna aiwatar da bincike a sassan kasar nan kan yadda za a farfado da shugabancin nagari mu tsara a rubuce, kuma mu gabatar ga jihohi da niyyar nemo maslaha.
Na biyu, mun lura ba a aiwatar da dokoki ko shirye-shiye yadda ya kamata. Don haka, muna fatar fahimtar da jama’a ta yadda za a samu hada hannu tsakanin hukumomin tsaro da jama’ar kasa duk lokacin da aka kafa doka wani ya taka jama’a su sanar da jami’an tsaro cewa ga wani ya taka doka don su kama shi su gabatar da shi gaban kotu ta hukunta shi.
Aminiya: Ko akwai wani abin da kuka yi don nemo mafita game da rikicin siyasa?
A kokarinmu na nemo maslaha kan rikice-rikicen siyasa, mun dauki wata hudu muna bincike kan me ya jawo tashin hankalin bayan zaben shekarar 2011, inda muka gano cewa, romo da ake samu in an hau mulki da kudin da ake kashewa wajen neman mulkin na daga cikin dalilan rikice-rikicen siyasa a kasar nan. Mun gano cewa muddin mutum zai dauki motar bas 10 zuwa 15 domin zuwa yakin neman zaben ciyaman ko dan majalisa, kuma kowace mota ta dauki mutum 18 da kowane matashi za a ba shi alawus da kwaya da makami, ba karamin kudi za a kashe ba.
To irin wadannan matasa da suka bugu da kwaya ko sholisho da sauransu, suna haduwa da abokan adawa sai fada ya barke, su rika sarar juna da makami. Na biyu galibi kuma wadannan matasa idan zabe ya wuce watsi ake yi da su bayan sun saba da rike makamai, sun saba da shan kwaya sun saba da samun kudin banza. To irinsu ne suke komawa ’yan sara-suka ko ’yan daba ko ’yan kalare su kafa kungiyoyi na cin zarafin jama’a.
Don haka mafitar da muka gano ita ce a haramta wa ’yan siyasa yawo da jama’a yayin kamfe. dan takara ya sanar da shugabannin jam’iyya su tara masa mutanen gari ko unguwar da zai je, ya je can ya same su ya gabatar musu da kudirorinsa ya koma inda ya fito, ba sai ya je musu gari ko unguwa da dandazon jama’a ba. Kuma ya ci gaba da kamfe ta hanyar kafafen watsa labarai ko ganawa da jama’a gida-gida daga lokaci zuwa lokaci, amma a yi kwambar motoci ana yawo gari-gari bai dace ba. Wannan zai sa wanda ya cancanci shugabancin jama’a amma ba ya da kudi, ya iya fitowa takara jama’a su zabe shi, kuma hakan zai sa a samu shugabanci nagari, zaman lafiya ya dore kasa ta ci gaba.
Aminiya: Me kuke yi don ceto matasa wadanda da su ’yan siyasa ke amfani wajen tayar da zaune-tsaye?
Akwai ayyukan da muke yi don amfanin matasa, kamar samar musu da hanyoyin koyon sana’o’i. Misali muna hada hannu da Cibiyar Koyar da Sana’o’i ta kasa da ke nan Abuja, inda akalla daga kafuwarmu muka nemo mutane daga jihohi takwas, kungiyarmu ta tallafa wa matasa 75 aka koyar da su sana’a a cibiyar. Sannan mun ziyarci gidajen kurkuku, inda muka gano ya kamata a gayyato masu hannu da shuni su rika tallafa wa gidajen da kayan abinci. Kuma mun yi haka a gidajen kurkuku na Suleja da na Nasarawa da na Zariya da na Katsina, inda muka hada hannu da wani dan kasuwa mai suna Alhaji Sa’idu Bello wajen tallafa musu. Kuma am irin wannan ziyyara ce muka yanke shawarar kungiyarmu ta dauki nauyi Cibiyar Koyar da Sana’o’i ta Abuja ta rika koyyar da fursunoni sana’o’i a gidajen kurkukun, kuma insha Allahu nan da wata biyu muke sa ran fara hakan a kurkukun Kaduna da Katsina da Zamfara da Nasarawa da Suleja da Zariya.
Don haka muna kira ga shugabanni da’yan kasuwa da masu zuciya, su mike tsaye wajen kyautata rayuwar wadanda suke tsare a koya musu sana’o’in da za su dogara da su ta yadda in sun fito za su samu ingancin rayuwa su zamo mutane nagari.
Aminiya: Ta ina kuke samun kudin gudanar da ayyukan kungiyar?
Mun dora wa mu kanmu shugabannin kungiya wani haraji don tafiyar da harkokinta. Kuma muna bayar da tallafi a tsakaninmu. Ba mu fara nemna taimako ko tallafi daga wasu kungiyoyi ba, amma wani lokaci gwamnati kan taimaka a ayyukan da suka shafe ta, kamar taron da muka yi ranar 19 ga Disambar 2012 kan tsaro da kyakkyyawan shugabanci, inda ta ba mu wurin gudanar da taron da tallafin alawus ga mahalartarsa.