✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Bunkasa harkokin kasuwanci ne zai magance matsalar tsaro’

Wani dan kasuwa da ke sayar da gwala-gwalai a babbar kasuwar Central da ke Jihar Bauchi, Alhaji Adamu Sifika ya shawarci gwamnan jihar da ya…

Wani dan kasuwa da ke sayar da gwala-gwalai a babbar kasuwar Central da ke Jihar Bauchi, Alhaji Adamu Sifika ya shawarci gwamnan jihar da ya ba da fifiko wajen bunkasa harkokin kasuwanci domin akwai dimbin ‘yan kasuwa da suka samu karayar arziki sakamakon matsalar tsaro da ya addabi yankin Arewa-maso-Gabas.
dan kasuwar  ya kara da cewa ya shafe sama da shekaru 25 yana kasuwanci a jihar kuma tsohuwar gwamnatin Isa Yuguda ta ba da basussuka ga wasu daga cikin ‘yan kasuwan, amma tun da yanzu an samu sabuwar gwamnati a kasar nan muna fatan nan da lokaci kadan kowa zai fara walwala.
Ya ce: “Talakawa da ’yan siyasa da ma’aikata kowa ya zuba ido ga sabuwar gwamnatin Najeriya tun da APC aka yi tun daga kasa har sama muna fatan za su ba da fifiko wajen shimfida ayyukan alheri ga al’umma. Adalci shi ne hanya daya tilo da zai magance matsalar tsaro a wannan yanki na Arewa-maso-Gabas idan aka samar wa matasa hanyoyin samun kudin shiga tabbas kasar nan za ta samu kwanciyar hankali.”
A karshe ya bayyana cewa a matsayinsu na ‘yan kasuwa suna fatan gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi za su kara wa  ma’aikatan gwamnati albashi domin “kowa ya san cewa idan ma’aikaci ya samu kudi to kasuwa zai je,” inji shi.