Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Juma’a da Litinin masu zuwa a matsayin hutu domin bukukuwan Easter na bana.
Mabiya addinin Kirista ne dai kan yi bukukuwan na Easter don tunawa da rataye Annabi Isah (A.S).
- Shugaban APC Abdullahi Adamu ya sauka daga kujerarsa ta Sanata
- Shin akwai bambanci tsakanin Buhari da Osinbajo?
Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da haka a madadin Gwamnatin Tarayya cikin wata sanarwa ranar Takara.
Sanarwar, wacce ke dauke da sa hannun Babban Sakataren ma’aikatar, Dokta Shu’aib Belgore, ta ce Ministan ya bukaci Kiristoci da su yi amfani da lokacin wajen koyi da halayen Annabi Isah (A.S) kamar su sadaukarwa, yafiya, tausayi, son zaman lafiya da hakuri.
Aregbesola ya kuma roke su da su yi wa Najeriya addu’a kan kalubalen tsaron da ke fuskantar dukkan sassanta.
Ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin za ta ci gaba da yin iyakar kokarinta wajen magance matsalolin yawan kai hare-haren a manyan hanyoyi da titunan jiragen kasa.
“Sha’anin tsaro abu ne da ya shafi kowa. Saboda haka, muna kiran ’yan Najeriya da ma ’yan kasashen waje mazauna kasar da su ci gaba da nuna tsantsar kishin kasa a wannan mawuyacin lokacin da kasar ke ciki ta hanyar tallafa wa yunkurin jami’an tsaro wajen dawo da zaman lafiya.