Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya shiga mahaifarsa birnin Ilorin a ranar Asabar.
Rabon Saraki da shiga Ilorin tun bayan faduwarsa zabe a 2019, lokacin da ya nemi konawa kujerarsa ta Sanatan Kwara ta Tsakiya.
- Sarkin Musulmi ya ce a duba sabon watan Rabi’ul sani
- Kwamishina ya kashe N25m wurin daukar nauyin auren zaurawa a Zamfara
- Najeriya ta kashe $6bn wurin shigo da alkama —Minista
Ya ziyarci mahaifar tasa ce don halartar taron addu’ar fidda’un cika shekara takwas da rasuwar mahaifinsa Olushola Saraki, da kuma bikin murnar cika shekara takwas da nada sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattaan ya samu gagarumar tarba daga dubban magoya bayansa a filin jiragen sama na Ilorin.
Daga nan magoya bayan sun raka shi har Fadar Mai Martaba Sarkin Ilorin.
Bayan nan ya ziyarci gidansu a mahaifarsa, inda babban limamin Ilorin, Alhaji Muhammad Bashir ya jagoranci gabatar da addu’o’i.
An ga ‘yar uwarsa kuma Minista a Ma’aikatar Sufuri, Gbemisola Saraki a wurin addu’ar.
Saraki, ya fadi zaben sake neman kujerar sanata ne ranar 23 ga watan Fabrairu 2019, karkashin inuwar jam’iyyar (PDP), inda ya samu kuri’a 68,994.
Abokin karawarsa na jam’iyyar APC, Ibrahim Oloriegbe ya kayar da shi da kuri’a 123,808.