Kungiyar kasashe masu fitar da danyen man fetur ta OPEC ta ce duk da kalubalen motoci masu amfani da wutar lantarki da kuma adadin lokacin da kasashe suka sanya na daina amfani da motoci masu amfani da man fetur, albarkatun man fetur sun kasance abin dogaro ga daukacin kasashen duniya.
Kungiyar OPEC wacce ba ta damu da juyin-juya-halin da ke aukuwa a duniyar na’urori masu yin amfani da wutar lantarki ba ta ce man fetur zai ci gaba da zama abin dogoro har zuwa shekarar 2040.
Kungiyar a mukalar da ta fitar ta shekarar 2017 a birnin Viyana ta yi hasashen cewa bukatar duniya na amfani da man fetur za ta karu zuwa ganga miliyan 111 da digo 1 a rana in shekarar 2040.