✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai yi balaguro zuwa Qatar

Buhari zai wuce birnin Doha kai tsaye daga Jihar Katsina.

Shugaba Muhammadu Buhari zai yi balaguro zuwa Qatar a yau Asabar, domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya.

Taron wanda shi ne na biyar a tarihi zai gudana ne game da abin da ya shafi kasashe masu karancin ci gaba wanda za a yi a Doha, babban birnin Qatar.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Malam Garba Shehu ya fitar, ya ce wannan ya biyo bayan sakon gayyatar da Sarkin Qatar, Sheik Tamim bin Hamad al Thani ya turo wa Buhari.

Fadar Shugaban Kasa ta ce Buhari zai wuce birnin Doha kai tsaye daga Jihar Katsina, inda ya tafi hutun jefa kuri’arsa ta zabe.

Taron wanda za a yi tsakanin 5 zuwa 9 ga watan nan an yi masa take ne da: “Daga Kasa Mai Yiwuwar Ci gaba Zuwa Mai Habaka” ana gudanar da shi ne sau daya cikin shekara 10.

Wata dama ce ga kasashe masu tasowa su samu taimako daga kasashen duniya domin samun cimma muradan karni cikin gaggawa kuma su taimaka musu wajen samun ci gaba.