✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi taron zaman lafiya a kasar waje

Buhari kai ziyarar aikin ne sa'o'i kadan bayan jawabinsa ga ’yan Najeriya kan sauyin kudi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Habasa domin halartar taro kan tsaro da zaman lafiya a kasashen Afirka.

Fadar Shugaban Kasa ta ce a yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai halarci taron tattaunawa kan matsaloli da ke addabar kasashen yammacin Afirka, tare da shugabannin kasashen.

Zai kuma halarcin zaman shugabannin kasashen ECOWAS, kuma zai gabatar da jawabai, kafin daga bisani ya dawo Abuja ranar Litinin.

Buhari kai ziyarar aikin ne sa’o’i kadan bayan jawabinsa ga ’yan Najeriya kan sauyin kudi, inda ya kara wa’adin amfani da tsoffin takardun N200 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu.

Ya kuma ba amince a ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200 kafada-da-kafada da sabbin N200, N500 da N1,000 zuwa ranar 10 ga watan Afrilu da tsoffin N200 za su daina aiki.

A cewarsa, zai ci gaba da lura da yadda tsarin sauyin kudin ke tafiya domin kada ya jefa ’yan Najeriya cikin kunci na babu gaira, babu dalili.

Ya bayyana cewa CBN zai ci gaba da aiki domin tabbatar da ’yan Najeriya na samun tsabar kudi ta hannun bankuna.

A halin da ake ciki, wasu gwamnoni sun maka CBN da Gwamnatin Tarayya a Kotun Koli kan sauyin kudin.

Kotun ta sanya 22 ga watan Fabrairu domin ci gaba da shari’a bayan ta dage lokacin aiwatar da wa’adin CBN na daina amfani da tsoffin kudin ranar 10 ga watan Fabrairu.