✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai tafi Senegal jim kadan bayan Harin Kuje

Zai kai ziyarar aiki kasar Senegal, jim kadan bayan ya sauya ministocinsa washegarin harin da aka kai wa ayarin motocinsa

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasa Senegal, jin kadan bayan ya sauya ministocinsa ya kuma rantsar da sabbi.

Tafiyar tasa na zuwa ne kasa da awa 24 bayan harin da aka kai wa ayarin motocinsa a mahaifarsa, Daura, Jihar Katsina.

Saudiyya ta kara wa Najeriya wa’adin jigilar Aikin Hajji

Babu dan Boko Haram ko daya da ya rage bayan harin Kuje —Ministan Tsaro

A jihar ce kuma ’yan bindiga suka kai wani harin kwanton bauna, inda uska kashe wani dan sanda mai mukamin Mataimakin Kwamishina.

A ranar cewa kuma wasu mahara suka kai hari a Gidan Yarin Kuje da ke Abuja, suka saki fursunoni kimanin 600.

Ministan Tsaro, Bashir Magashi, ya bayyana cewa manyan mayakan Boko Haram kusan 64 da ke tsare a gidan yarin sun yi batar dabo bayan harin na ranar Talata da dare.

Sanarwar da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar ta ce ranar Alhamis Buhari zai yi wata ganawa da Shugaba Macky Sall na Senegal da shugabannin sauran kasashe kan hayoyin da kasashe za su farfado daga tasirin COVID-19 da kuma shawo kan matsalar tsaro da ke ci musu tuwo a kwarya.

Wani abin da za su tattauna a kai shi ne tasirin yakin Rasha da Ukraine a kan tattalin arzikin kasashen.

%d bloggers like this: