✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai tafi Liberia ranar Talata

Liberia ta cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai daga masu mulkin mallaka

Shugaba Muhammadu Buhari na shirin balaguro zuwa Liberia, inda zai gabatar da jawabi kan matsalar tsaro a yankin Yammacin Afika da gudanar da sahihin zabe da kuma mutunta doka.

A gobe Talata ne, shugaban zai kama hanyar zuwa kasar ta Liberia kamar yadda sanarwar da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar ta bayyana.

Buharin zai hadu da wasu takwarorinsa na kasashen Afrika a birnin Monrovia a daidai lokacin da kasar ta Liberia ke bikin cika shekaru 175 da samun ‘yancin kai daga masu mulkin mallaka.

Tawagar Buharin za ta kunshi Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffery Onyeama, da kuma Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i.

Balaguron da Buharin zai yi na zuwa ne akalla kwanaki biyu da ‘yan ta’adda suka saki wani hoton bidiyo da ke nuna yadda suke azabtar da fasinjojin jirgin kasan da suka yi garkuwa da su akan hanyar Abuja-Kaduna.

A cikin bidiyon dai, ‘yan ta’addar sun yi barazanar sace shugaba Buhari tare da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i.