Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja ranar Alhamis domin wata ziyarar kwana hudu zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
Zai je kasar ne domin halartar taron Shugabannin Kasashe na Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), karo na 35.
- ’Yan ci-rani 12 sun daskare a dusar kankara a kokarinsu na shiga Turai
- ’Yan bindiga sun hallaka mutum 40 a sansanin ’yan gudun hijirar kasar Kongo
A cewar wata sanarwa ta bakin mai magana da yawun Shugaban, Femi Adesina, Buhari, yayin tafiyar, zai samu rakiyar Ministocin Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama, da na Lafiya, Osagie Ehanire, da na Noma, Mohammed Abubakar, da ta Jinkai da Walwalar Jama’a, Sadiya Umar-Farouk.
Sauran ’yan tawagar Shugaban sun hada da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Najeriya (NIA), Ambasada Ahmed Rufa’i.
Sanarwar ta ce, “Shugaba Buhari zai bi sahun sauran Shugabannin Afirka domin tattauanwa wajen lalubo bakin zaren matsalolin da ke ci wa nahiyar Afirka tuwo a kwarya a bangaren siyasa da tattalin arziki da kuma zamantakewa.
“Taken taron na bana shi ne ‘Aza harsashin inganta cimaka, samar da abinci da zaman lafiya a nahiyar Afirka: Bunkasa noma, habaka ci gaban dan Adam, zamantakewa da tattalin arziki’.
“A gefen taron kuma, Shugaba Buhari zai tattauna da wasu shugabanni a kan hanyoyin habaka cinikayya a tsakaninsu, hadin gwiwa don magance kalubalen tsaro da kuma inganta dangantaka tsakanin Najeriya da sauran kasashe,” inji sanarwar.