Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata zai tafi Belgium don halartar taron hadin gwiwa tsakanin kungiyar hadin kan Afirka ta African Union (AU) da takwararta ta Tarayyar Turai (EU).
Taron wanda zai gudana a birnin Brussels daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu.
- Rikicin Tigray: An janye dokar ta-baci a kasar Habasha
- Kungiyar Dalibai za ta shiga zanga-zanga kan yajin aikin ASUU
Wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta ce ana sa ran Buhari zai dawo gida Najeriya ranar Asabar.
Daga cikin tawagar shugaban kasar akwai Ministan Harkokin Waje, Ambasada Geoffrey Onyeama; Ministan Lafiya, Dokta Osagie Ehanire da Karamin Ministan Muhalli, Sharon Ikeazor.
Sauran yan tawagar kuma akwai Mai ba da Shawara kan Harkokin Tsaron Kasa, Manjo Janar Babagana Monguno, Shugaban Hukumar Leken Asiri, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar da Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare, Abike Dabiri.
Sanarwar wacce mi magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya sanya wa hannu, ta ce shugaban zai yi amfani da damar wajen tattauna sauran al’amura da wasu kasashe.
Abubuwan da shugabannin za su tattauna sun hada da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.