Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi birnin New York na Amurka ranar Lahadi domin halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 76.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin Shugaban Kasar, Femi Adesina ya fitar a Abuja ranar Asabar.
- Karnukan mai makaranta sun yi kalaci da dalibi a Anambra
- ‘Yadda ’yan bindiga suke karbar haraji daga gare mu’
A cewarsa, Shugaban zai sami rakiyar Ministocin Harkokin Waje da na Shari’a da kuma ta Muhalli.
Har ila yau, tawagar Shugaban za ta kunshi mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da Shugaban Hukumar Leken Asiri ta Kasa (NIA) da Shugabar Hukumar Kula da ’Yan Najeriya Mazauna Ketare da kuma Mai Taimaka Masa Kan Cimma Muradun Karni (MDGs).
Adesina ya kuma ce yayin ziyarar, Shugaba Buhari zai yi jawabi ga Babban Zauren Majalisar ranar Juma’a, inda ake sa ran zai yi magana a kan jigon taron wanda zai mayar da hankali kan farfado da tattalin arzikin duniya daga annobar COVID-19, da sauran batutuwan da suka shafi kasa da kasa.
Kazalika, tawagar ta Najeriya za ta halarci wasu tarukan da dama musamman bangaren samar da abinci da makamashi da kuma makamin Nukiliya.
Ana kuma sa ran Shugaban zai tattauna da takwarorinsa na wasu kasashen kan hanyoyin bunkasa hulda da juna.
Sanarwar ta ce ana sa ran dawowar Shugaba Buhari da tawagarsa zuwa Najeriya ranar Lahadi, 26 ga watan Satumbar 2021.