✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai soke aikin jirgin kasa da ya bai wa kamfanin CCECC

Ministan Sufuri ya bai wa kamfanin kasar China wa'adin wata biyu saboda tafiyar hawainiya

Gwamnatin Tarayya za ta soke kwangilar aikin jirgin kasa da ta bai wa kamfanin CCECC na kasar China.

Ministan Sufuri, Muazu Sambo, ya ce gwamanti na duba yiwuwar soke kwangilar ce saboda kwamfanin ya ki ba da kashi 85 cikin 100 na kudaden da aka yi yarjejeniya zai bayar domin aiwatar da aikin.

“Na ba su wa’adin watan Oktoba 2022 su cika nasu bangaren alkawarin ko kuma su fuskanci hukunci mai tsauri,” in ji shi.

“Ya za a yi a ce yau shekara biyu da sanya hannu a kan yarjejeniyar, amma CCECC bai bayar da ko sisi ba,” in ji shi.

Ya bayyana cewa yarjejeniyar da aka kulla ita ce kamfanin zai bayar da kashi 85 cikin 100 na kudin aikin, Gwamnatin Tarayya kuma za ta ba da kashi 15 cikin 100.

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Asabar, lokacin da ya kai ziyar gane wa kansa yanayin aikin da ake gudanarwa a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Legas, a ranar Asabar.