Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta amince da nadin tsaffin manyan hafsoshin soji da ya sallama a makon jiya a matsayin jakadun Najeriya.
Sanarwar hakan tana kunshe cikin wani sako da hadimin shugaban kasar na shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad ya wallafa da Yammacin ranar Alhamis a shafinsa na Twitter.
- Buhari ya tsawaita wa’adin Shugaban ’yan sanda
- Coronavirus ta yi ajalin wani tsohon dan Majalisar Kano
- Abin da ya sa Ganduje ya rufe masallacina —Sheikh Abduljabbar
Hadimin shugaban kasar ya ce an aike da sunayen tsaffin manyan hafsoshin sojin da suka yi ritaya zuwa Majalisar Dattawan Najeriya da zummar nada su a matsayin jakadu ga kasar a wasu kasashe na ketare.
Malam Bashir ya ce tsaffin manyan hafsoshin sojin da da aka aike wa Majalisar Dattawan sunayensu sun hadar da Janar Abayomi Olanisakin da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas.
Sauran sune Laftanar Janar Tukur Buratai da Air Marshal Sadique Abubakar da kuma Air Vice Marshal Muhammad S Usman.