✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Buhari zai kashe wa kansa biliyan N24bn a 2022

Buhari zai kashe N1.5bn a tafiye-tafiye da kuma N331m a abinci da makulashe.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ware wa kansa Naira biliyan 24.835 domin kashewa a shekarar 2022.

Daga cikin kudaden da ake ware wa Ofishin Shugaban Kasa a kasafin 2022, Buhari zai kashe Naira biliyan 2.309 wajen yin tafiye-tafiye a shekarar.

An kuma ware Naira miliyan 301 na cin abincin Shugaban Kasa, sai kuma Naira miliyan 30.6 na kayan tande-tandensa.

Tafiye-tafiya Buhari zuwa kasashen waje za su ci Naira biliyan 1.5, sai tafiye-tafiyen cikin gida da za su ci Naira miliyan 775.602.

An kuma ware Naira biliyan 21.975 domin yin gine-gine, ciki har da bangaren Shugaban Kasa da ake ginawa a Asibitin Fadar Shugaban Kasa.

Akwai kuma Naira miliyan 174.176 da aka ware domin biyan alawus din mahalarta taro da kuma kyaututtuka.

Sanarwa da tallace-tallacen Fadar Shugaban Kasa za zu ci Naira miliyan 41.219, sai tura sakonni da kudin sayen takardar kan sarki Naira miliyan 4.788.