Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabbin takardun kudi da aka sauyawa fasali a ranar Laraba, 23 ga watan Nuwamba, 2022.
Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ne ya tabbatar da hakan a yayin taron Kwamitin Kudi na Kasa da aka saba gudanarwa wata-wata a Abuja.
- ‘Yan sanda biyu sun rasu, 17 sun jikkata a hatsarin mota a Filato
- Qatar 2022: Saudiyya ta lallasa Argentina a Gasar Cin Kofin Duniya
Ana iya tunawa cewa, a watan Oktoba ne Emefiele ya bayyana cewa Babban Bankin Kasar zai sauya wa takardun kudi na N200, N500 da kuma N1,000 fasali daga ranar 15 ga Disamba, 2022.
Emefiele ya bayyana cewa, CBN ba zai jira har zuwa watan Disamba ba don kaddamar da sabbin takardun kudin.
Sai dai ya ce ba za a sauya wa’adin karbar tsofaffin takardun kudin a bankuna ba a kokarin musanya su da sabbi.
Wannan sauyi na kudi ya jawo cece-kuce mai tarin yawa a tsakanin al’ummar kasar, wanda wasu ke ganin hakan na iya kawo koma baya ga tattalin arzikin kasa.
Wasu kuma na yabawa, amma sun ce shirin bai zo a lokacin da ya dace ba, domin hakan na iya jefa miliyoyin talakawa cikin halin ka-ka-ni-ka-yi.