Hukumar Samar da Kayayyakin Kimiyya da Injiniyanci ta Najeriya (NASENI) ta ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai kaddamar da jirgin sama mai saukar angulu irinsa na farko da kasar ta kera kafin ya bar mulki a 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mohammed Sani Haruna ne ya bayyana hakan a Kaduna ranar Talata.
- Kotu ta daure ’yan fashin babur shekara 28 a kurkuku
- An ceto mata masu juna-biyu 10 daga masana’antar kyankyasar jarirai a Ribas
Ya yi alkawarin ne jim kadan bayan ya kai wa Kwamandan Makarantar Fasaha ta Rundunar Sojin Najeriya (AFIT), AVM Paul Jemitola, ziyara a Kaduna.
Farfesa Mohammed ya kuma ce ya kai ziyarar ce a wani bangare na duba yadda aikin jirgin ke gudana.
A cewar Shugaban na NASENI, tuni aka hada wasu jiragen guda biyu a nan gida, yayin da wani wanda aka kera komai nashi a Najeriya ake kan kammala shi yanzu haka.
Shugaban ya ce, “Idan komai ya tafi daidai, Shugaban kasa zai kaddamar duk abin da aka sami kammalawa kafin ya bar ofis ranar 29 ga watan Maris din 2023.”
AFIT, wacce wani bangare ce na Rundunar Sojin Sama ta Najeria da kuma NASENI ta sha alwashin kera jirgin karo na farko a tarihin Najeriya.
Tun da farko, Kwamanda AVM Paul ya bayyana jin dadinsa da aikace-aikacen hukumar ta NASENI, inda ya ce a shirye suke su yi aiki tare kafada da kafada.