A ranar Litinin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai kaddamar da sabuwar Tashar Ruwa ta Tsandauri ta Dala a Jihar Kano.
Babban Daraktan Tashar, Ahmad Rabi’u ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
- Kashi 70 na ’yan Najeriya na amfani da maganin gargajiya —NNMDA
- Kotu ta ayyana Oyetola a matsayin Gwamnan Osun
A cewarsa, shirye-shirye sun kammala don kaddamar da sabuwar tashar da ke Zawaciki a Karamar Hukumar Kumbotso.
Rabi’u ya ce tashar ruwan ta kan tudu ta kasa-da-kasa ce kuma irinta ta farko da za ta dinga kwasar kaya daga Kano zuwa sauran sassan duniya.
Ya kara da cewa, duk da tashar ta kai fadin kadada shida, za a ci gaba da fadada ta idan bukatar hakan ta taso.
Rabi’u ya ce dukkanin abubuwan da ’yan kasuwa ke bukata don fitar da kayayyakinsu, da tantancewar Hukumar Kwastam, za a yi shi ne daga Kano.
A nasa bangaren, Shugaban Tashar ta Dala Alhaji Abubakar Bawuo cewa ya yi an samar da tashar ce domin bunkasa kasuwanci a Jihar Kano, kasancewarta cibiyar hada-hadar kasuwanci a Najeriya da ma nahiyyar Afirka baki daya.