✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai kaddamar da aikin shekara 40 a Katsina

Bayan shafe shekara 40 da fara aikin Buhari zai kaddamar da shi a ranar Alhamis.

A ranar Alhamsi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da madatsar ruwa ta Zobe, tare da aikin titin garin Dutsinma zuwa Tsaskiya mai tsawon kilomita 50.

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai jami’n Gwamna Anminu Masari na Jihar Katsina, Abdu Labaran Malumfashi.

  1. Gwamnati za ta tallafa wa Almajirai 12,000 a Yobe
  2. Dalilin da APC ta fadi zaben wasu jihohi a 2019 —Buhari

Aikin madatsar ruwan ta Zobe da aikin titin Dutsinma zuwa Tsaskiya, dukkansu na Karamar Hukumar Dutsinma a jihar Katsina, wanda gwamnatin tarayya da ta jiha suka dauki nauyin yi.

“Aikin madatsar ruwan Zobe na biliyoyin kudade an faro shi tun a 1980 a lokacin mulkin Shugaba Shehu Shagari, amma an kammala shi a lokacin APC a karkashin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

“Titin Dutsinma zuwa Tsaskiya mai tsawon kilomita 50 kuma an kirkire shi a 2017 a karkashin Gwamna Aminu Bello Masari,” a cewar sanarwar.