Gwamnatin Tarayya ta ce ta kammala shirye-shiryen gina gidaje 10,000 masu saukin kudi a Jihar Kano, don inganta samar da gidaje ga ’yan Najeriya.
Manajan-Daraktan Hukumar Kula da Gidaje ta Tarayya (FHA) Sanata Gbenga Ashafa, ya bayyana hakan yayin duba fili mai fadin kadada 500 da Gwamnatin Jihar Kano ta ware don aikin a garin Dawanau na Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar.
- Buhari ya nada dan shekara 40 a matsayin sabon Shugaban EFCC
- Abudlrasheed Bawa: Yadda Majalisa za ta tantance sabon Shugaban EFCC
- Abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da sabon shugaban EFCC
Ashafa, wanda Babban Daraktan Ci Gaban Harkokin Kasuwanci na hukumar, AbdulMumin Jibrin ya wakilta ya ce aikin na daga cikin shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya da nufin magance matsalar karanci gidaje a kasar.
Ya ce Hukumar ta fara shirye-shirye masu inganci na gyara Gidajen Gwamnatin Tarayya a fadin kasar, sannan ta tura ma’aikata zuwa shiyyar Arewa maso Yamma don aiwatar da ayyukan nata da sauri.
Da yake yaba wa Gwamna Abdullahi Ganduje kan filin da ya bayar, Ashafa ya bukaci ma’aikatan Hukumar da su nuna kwarewa da kwazo wurin yin ayyuka masu inganci.