✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai gana da Shugabannin Tsaro

Ganawarsa da su ta farko bayan dawowarsa daga Birtaniya.

Shugaban Kasa Muhammad Buhari zai yi zama da shugabannin tsaro na kasar nan, a karon farko bayan dawowarsa daga kasar Birtaniya, inda ya halarci taron ilimi na duniya ya kuma ga likita.

Ganawar na zuwa ne bayan dakarun gwamnati sun shafe makonni suna tsananta kai hare-hare kan maboyan ’yan kungiyar Boko Haram har suka yi ta mika wuya.

Sanarwar da Fadar Shugaba Kasa ta fitar ta ce Buhari zai yi zmaa da shugabannin tsaro a ranar Alhamis, inda za su yi masa bayanin inda aka kwana a kokarinsu na murkushe ayyukan Boko Haram da ’yan bindiga da dangoginsu.

Sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Femi Adesina ya fitar ranar Talata ta ce, zaman zai kuma tattauna kan wasu matsaloli da hukumomin suke fuskanta tare da lalubo musu mafita.

Shugabannin tsaro da za su halarci taron sun hada da Mashawarchin Shugaban Kasa kan Tsaro, Babagana Monguno; da Babban Hafsan Tsao, Laftanar Janar Lucky Irabor; da Manyan Hafsoshin Sojin Kasa da na Sama da na Ruwa; da Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya; da sauransu.