A gobe Talata ake sa ran Shugaba Muhammadu Buhari zai yi wata ganawa ta musamman da Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, ganawar za ta gudana ne ta kafar intanet.
- An rage wa ma’aikaci albashi saboda dadewa a bandaki
- ’Yan bindiga sun kashe DPO da jami’ansa takwas a Kebbi
Sanarwar da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Ned Price ya fitar ta ce, ganawar Shugaba Buhari da Mista Blinken za ta mayar da hankali ne kan al’amuran da suka shafi cinikayya da annobar Coronavirus.
Kazalika, sakataren harkokin wajen zai kuma gana da Shugaban Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da sakatariyarsa, Raychelle Omamo.
“A gobe Talata, 27 ga watan Afrilu, Mista Blinken zai yi ganawarsa ta farko da Shugabannin Afirka biyu, inda zai gana da Shugaban Najeriya da kuma na kasar Kenya.
“Yayin ganawarsu, Mista Blinken zai gana da Shugaba Buhari da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Geoffery Onyeama domin inganta alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Aminiya ta fahimci cewa, wannan dai ita ce tattaunawa ta farko da Mista Blinken zai yi da shugabannin Afirka a gwamnatin Shugaban Amurka, Joe Biden.