✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai gabatar da kididdigar masu kanjamau a Najeriya a wannan wata – Dokta Aliyu

A cikin wannan wata ne ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da sakamakon bincike don kididdige masu dauke da cutar kanjamau da Hukumar…

A cikin wannan wata ne ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da sakamakon bincike don kididdige masu dauke da cutar kanjamau da Hukumar Yaki da Cutar Kanjamau ta Kasa (NACA) ta gudanar a sassan kasar nan.

Darakta Janar na Hukumar NACA, Dokta Sani Aliyu ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da Aminiya a Abuja, inda y ace kididdigar wadda gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin Dala miliyan 90 don gudanar da ita an sanya mata sunan “Kididdigar Ma’aunan Kanjamau da kuma Illarta ta Najeriya (NAIIS), kuma ita ce irinta mafi girma da aka gudanar a duniya, sannan Najeriya ce kasa ta 12 da ta gudanar da ita.

Dokta Sani Aliyu ya ce, “Za a gabatar da sakamakon kididdigar ce a wannan wata na Maris a wani bangare na bikin da muke niyyar gabatar da wani kundi da zai zamo jagora ga tsare-tsaren yadda za a magance annobar cutar kanjamau. Abokan hadin gwiwarmu ma za su kara gusawa gaba zuwa wannan hanya. Muna da jihohin da suke da matakai daban-daban na cutar kanjamau fiye da yadda muke zato da kuma akasin haka. Kuma mun gano inda ya kamata mu kara mayar da hankali.”

Ya ce kididdigar wadda ta gudana ta hanyar samfurin gida-gida ta bayyana yadda ake fama da kanjamau da cutar hanta rukunin Hepatitis B da C a kasar nan, tare da auna yadda ake gudanar da ayyukan magance cutar kanjamau a tsakanin wadanda suka fi saurin kamuwa da ita da kuma kiyasta yadda hadarin kamuwa da ita yake a tsakanin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Shugaban Hukumar NACA, ya kara da cewa: “Dalilin da ya sa muka yanke shawarar yin wannan aiki tare da abokan hadin gwiwarmu shi ne muna fuskantar babban kalubale kan gano hakikanin adadin mutanen da suke dauke da cutar kanjamau a kasar nan.”

Ya ce, kididdigar za ta bai kasar nan damar magance matsalolin cutar kanjamau yadda ya kamata, “Shirin NAIIS, babu shakka shi ne babbar shaidar da muke da ita cewa idan ka yi shiri sosai ka san bayanan da suka dace za ka iya magance matsalar. Amma idan ba ka san bayanan da suka kamata ba, abin da za ka rika yi shi ne shaci-fadi kawai,” inji shi.

Ya ce kididdigar ta duba halin da cututtuka uku suke ciki ne da suka hada da: illar kanjamau da ciwon hanta na rukunin Hepatitis B da C.

Dokta Aliyu ya ce duk da cewa kanjamau tana ci gaba da zama babbar cutar da ke jawo mace-mace a Najeriya, “Amma a hakika ciwon hanta ma wata babbar matsala ce ga kiwon lafiyar jama’a. Adadin mutanen da suke mutuwa dalilin ciwon hanta da rukunin Hepatitis B ko C ke jawo a Najeriya ya fi na wadanda kanjamau take jawowa,” inji shi.

Ya ce, “Kididdigar za ta bayana “irin nauyin kanjamau da muke fama da ita. Kuma za ta shaida mana jimillar mutanen da suke karbar maganinta idan aka hada da wadanda ya kamata a ce suna karbar maganin.”