✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari zai gabatar da daftarin kasafin kudi a ranar Alhamis

A ranar Alhamis ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2021 a gaban zaman tare na Majalisu biyu…

A ranar Alhamis ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, zai gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2021 a gaban zaman tare na Majalisu biyu na Dokokin Tarayya.

A cewar Ezrel Tabiowo, hadimi na musamman a bangaren yada labarai ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Ubangidansa a wata wasikar Shugaban Buhari da ya karanta yayin zaman Majalisar a ranar Talata.

Wasikar Shugaban Kasar ta ce: “Cike da karamci da girmama, ina neman alfarmar Majalisar Dattawa da bani dama da misalin karfe 11.00 na safiyar ranar Alhamis, 8 ga watan Oktoba, domin na gabatar da kudirin kasafin kudi na 2021a gaban zaman tare na Majalisun Tarayya biyu.

“A yayin da nake fatan yin jawabi a gaban zaman tare na Majalisun biyu, ina mai bai wa Shugaban Majalisar Dattawa tabbacin girmamawa ta.”

Tun a zaman Majalisar Dattawa na ranar Talata ta makon jiya, Sanata Ahmad Lawan a sakonsa na barka da dawo wa daga hutun shekara ga ‘yan majalisar, ya sanar cewa Shugaba Buhari zai gabatar da kasafin kudin kasar na shekara mai zuwa a gaban zaman tare na Majalisar Tarayyar kasar biyu a wannan mako.

Ana sa ran Shugaban Kasar zai gabatar da Naira Tiriliyan 13.08 a matsayin daftarin kasafin kudin kamar yadda ya amince yayin zaman Majalisar Zartarwa da aka gudanar a makon jiya.